Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-23 17:08:25    
Filin hilali na birnin Wuzhong

cri

Yau na je filin hilali na birnin Wuzhong da ke tsakiyar jihar Ningxia don yin intabiyu. Da zarar na shiga filin, sai gine-gine na halin musamman na Musulunci sun jawo hankalina sosai.

Filin hilali wata kasuwa ce wajen sayar da abincin musulmi da kayayyakin musulmi, wanda birnin Wuzhong ya gina shi domin raya tattalin arzikin kabilar Hui da kuma yada al'adun gargajiya na musulunci.

Lokacin da na shiga wani kanti mai suna "Yijin" da ke cikin kasuwar, wani musulmi yana sayen tufafi, kuma ya gaya mini cewa, tufafin da kantin ya sayar suna da inganci sosai, kuma sun dace da yanayin arewa maso yammacin kasar Sin. Kullum ya kan sayi kayayyaki daga kantin.

Muhimman kayayyakin da kantin Yijin ya sayar kayayyaki ne da aka yi tare da wata irin fatar tumaki ta birnin Wuzhong wadda ake kiranta "ermaopi".

Irin wannan fatar tumaki tana daya daga cikin kayayyakin musamman biyar na jihar Ningxia, wadda tana da launin fari, kuam tana da taushi. Bugu da kari kuma za a ji dumi sosai in an sa tufafin da aka yi tare da ita.

Shugaban kantin Yijin Ma Yun ya gaya mini cewa, a shekarar da muke ciki, yawan kudaden da ya samu wajen sayar da irin wadannan kayayyaki ya kai kusan kudin Sin wato Yuan miliyan 10. Dimbin mutanen da ke wurare daban daban sun zo kantin don sayar da fatar tumaki ta "ermaopi". Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ingancin tufafinsa yana da kyau. Ban da wannan kuma kantin ya sayar da fatar tumaki zuwa kasashe daban daban, musamman ma kasashen Turai da kasashen Amurka da Canada, kuma yawan kudaden da ya samu a wannan fanni ya kai kudin Sin wato Yuan miliyan 4 a shekarar nan.