Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-22 17:58:22    
An samu sakamako mai kyau wajen raya masana'antun kwal cikin hali mai dorewa a lardin Shanxi

cri

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, lardin Shanxi na kasar Sin ta samu sakamako mai kyau wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na raya masana'antun kwal cikin hali mai dorewa. An riga an rufe dimbin kananan masana'antun hako kwal da sauran masana'antun da suke da nasaba da kwal wadanda suka gurbata muhalli kuma suka yi amfani da makamashi masu dimbin yawa a lardin Shanxi.

Mr. Du Fuxin, wanda yake da shekaru 59 da haihuwa, shi ne shugaban rukunin kamfanonin kwal na lardin Shanxi. A cikin shekaru 6 da suka wuce, ya yi amfani da lokuta da yawa wajen saye ko yin kwaskwarima kan kanana ko matsakaitan masana'antun hako kwal. Mr. Du ya ce, "A cikin shekaru 3 ko 5 kawai da suka wuce, ingancin injuna da fasahohin hako kwal da na aiwatar da masana'antu sun samu cigaba sosai. Alal misali, mun kyautata tsarin sa ido kan gas da sauran ayyukan yau da kullum."

Lardin Shanxi lardi ne da ke samar da kwal mafi yawa a nan kasar Sin. Yawan adanannen kwal da aka gano a karkashin kasa ya kai fiye da ton biliyan 260, wato ya kai kashi 1 cikin kashi 4 bisa na dukkan kwal da aka gano a kasar Sin. A cikin dogon lokacin da ya wuce, manyan masana'antun hako kwal da gwamnatin kasar Sin take mallakar hannun jarinsu suna kasancewa tare da sauran matsakaita ko kanana masana'antun hako kwal. Injunan da ake amfani da su a cikin wadannan kanana ko matsakaita masana'antun hako kwal suna koma baya. A kullum suna haddasa hadaruruka a cikin irin wadannan masana'antun hako kwal. A farkon karnin da muke ciki, gwamnatin lardin Shanxi ta gabatar da manufar "rufe kananan masana'antun hako kwal, da kuma yin kwaskwarima kan matsakaitan masana'antun hako kwal tare da raya manyan masana'antun hako kwal". Saboda haka, an kafa wannan rukunin kamfanonin hako kwal na lardin Shanxi da ke karkashin shugabantar Du Fuxin a shekara ta 2001.

Bugu da kari kuma, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lardin Shanxi yana kokarin neman hanyoyin raya masana'antun hako kwal cikin hali mai dorewa. Alal misali, yanzu ana mayar da gas da aka samu daga masana'antun hako kwal da ya zama gas na girki, kuma ana amfani da dagwalon kwal wajen samar da wutar lantarki. Mr. Zhang Lichun, mataimakin shugaban kamfanin samar da wutar lantarki da dagwalon kwal na birnin Gujiao ya gaya wa wakilanmu cewa, "An kafa wannan kamfani ne domin yin amfani da dagwalon da ake samu daga masana'antar wanke kwal ta birnin Gujiao. A da, an zubar da wadannan dagwalo kawai, kuma suna gurbata muhalli. Amma yanzu mun dawo da su domin samar da wutar lantarki. Ba ma kawai za mu iya tsimin makamashi ba, har ma za mu iya kiyaye muhalli."

Bugu da kari kuma, manyan masana'antu ko kamfanoni na kwal na lardin Shanxi suna saye ko hada da kanana ko matsakaita masana'antun hako kwal ta hanyoyi iri daban-daban. An riga an rufe dimbin kananan masana'antu masu gurbata muhalli da suke samar da kwal kadan. Mr. Zhang Baoshun, sakataren reshen lardin Shanxi na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, lardin Shanxi yana kokarin kawo wa jama'a hakikanan moriya iir iri ta hanyar aiwatar da tunanin neman bunkasuwa ta hanyoyin kimiyya. Mr. Zhang ya ce, "Dole ne a nemi hanyoyin neman cigaba mai dorewa, wato kyautata canja hanyoyin neman cigaban tattalin arziki da raya tattalin arzikin bola jari da yin tsimin da kiyaye makamashi. A waje daya, a tsabtace muhallin da muke ciki, da kuma kara raya yanayi mai daukar sauti. Lokacin da muke neman sabon cigaba, dole ne mu yi kokarin kiyaye muhalli. Bugu da kari kuma, dole ne mu yi kokarin samar wa sauran yankunan kasarmu makamashin da suke bukata cikin hali mai dorewa, kuma kawo wa jama'ar lardin Shanxi fatan alheri da moriya a cikin dogon lokaci mai zuwa." (Sanusi Chen)