Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-20 16:37:46    
Bunkasuwar tufafin musulmi a jihar Ningxia

cri

Yanzu na shiga wata masana'antar samar da tufafin musulmi wadda ake kiranta "Wantini" da ke birnin Wuzhong da ke tsakiyar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin. Ana iya ganin cewa, ma'aikata masu dimbin yawa suna kokarin yin tufafin musulmi. Jihar Ningxia wata jiha ce da ake iya samun musulmai mafi yawa a duk fadin kasar Sin, shi ya sa kayayyakin musulmi suna samun bunkasuwa kwarai da gaske a jihar.

An kafa wannan masana'antar samar da tufafin musulmi na Wantini a shekara ta 1998 bisa goyon bayan gwamnatin birnin Wuzhong. Kuma a lokacin kaka na shekara ta 2005, gwamnatin birnin ta tsai da kudurin kara karfin goyon bayan bunkasuwar masana'antar, wato ta samar da wani sabon wuri babba ba tare da karbar kudade a yanzu ba, sai dai bayan ta iya gudanar da ayyukanta kamar yadda ya kamata.

Shugaban masana'antar yin tufafin musulmi na Wantini Yang Jinxiang ya gaya mana cewa, "dalilin da ya sa aka kira wannan masana'anta da sunan 'Wantini' shi ne sabo da wannan kalma ta zo daga Larabci, kuma ma'anarta ita ce samar da taimako ga sauran mutane. Shi ya sa masana'antarmu tana bin ka'idar tsayawa tsayin daka kan adalci, da samun bunkasuwar tattalin arziki, da raya ayyuka bisa bukatun mutane, da kuma gina zamantakewar al'umma mai jituwa."

A da, a kan yi tufafi da hannu, shi ya sa ba a iya samun tufafi da yawa a ko wace rana ba. Domin kara saurin samar da tufafi, masana'antar Wantini ta sayo na'urorin zamani 4 a shekara ta 2005, wadanda darajar ko wanensu ta kai kudin Sin wato Yuan kimanin dubu 15 . Ta haka, yawan tufafin musulmi da masana'antar take samarwa ya ninka sau da yawa. Wata ma'aikaciya ta gaya mana cewa, "Bayan da na yi amfani da wannan na'ura, na iya samar da huluna fiye da 800 a ko wace rana, a da, na iya samar da huluna 2 ko 3 kawai."

Haka kuma domin samun bunkasuwa tare da ci gaban zamani, masana'antar Wantini ta dauki masu zane-zanen tafafi domin su iya zana tufafin musulmi na sabon salo. Ma Zhi, shugaban ofishin kula da harkokin samar da tufafi na masana'antar ya gaya mana cewa, "a shekarar nan da muke ciki, mun dauko masu zane-zane biyu da suka gama karatunsu daga kwalejin koyon ilmin tufafi na birnin Xi'an na kasar Sin, su biyu da kuma wani tsohon mai zane-zane na masana'antarmu suna kula da ayyukan zayyana tufafin musulmi."

Sabo da yin amfani da na'urorin zamani da kuma samar da tufafi na sabon salo, masana'antar Wantini ta samu bunkasuwa cikin sauri. Yanzu dimbin baki 'yan kasuwa da ke shiyyar Gabas ta tsakiya suna sayen tufafin musulmi daga wurin. Har ma wasu 'yan kasuwa na kasar Sin sun fitar da tufafin da masana'antar ta yi a kasar Aljeriya.

Shugaba Yang yana cike da imani sosai ga makomar masana'antar. Kuma ya bayyana cewa, "masana'antar tana da wata kyakkyawar makoma, dalilin da ya sa na fadi haka shi ne sabo da kasashen Larabawa suna bukatar irin wadannan tufafi masu dimbin yawa. Kuma sabo da farashin tufafinmu ya yi arha, shi ya sa dole ne za su samu karbuwa sosai a shiyyar gabas ta tsakiya."

Bugu da kari kuma, shugaba Yang ya gaya mana cewa, ko da yake yanzu bai ci riba sosai daga wajen sayar da tufafin musulmi ba, amma yana ganin cewa, yada al'adun gargajiya na kabilar Hui ta hanyar sayar da tufafin musulmi zuwa wurare daban daban ya fi muhimmanci. (Kande Gao)