
Sabo da yin amfani da na'urorin zamani da kuma samar da tufafi na sabon salo, masana'antar Wantini ta samu bunkasuwa cikin sauri. Yanzu dimbin baki 'yan kasuwa da ke shiyyar Gabas ta tsakiya suna sayen tufafin musulmi daga wurin. Har ma wasu 'yan kasuwa na kasar Sin sun fitar da tufafin da masana'antar ta yi a kasar Aljeriya.
Bugu da kari kuma, shugaba Yang ya gaya mana cewa, ko da yake yanzu bai ci riba sosai daga wajen sayar da tufafin musulmi ba, amma yana ganin cewa, yada al'adun gargajiya na kabilar Hui ta hanyar sayar da tufafin musulmi zuwa wurare daban daban ya fi muhimmanci.(Kande) 1 2 3
|