
Mai yiwuwa ne a gun taron wasannin Olympic na shekarar 2012, a madadin kasar Sin, Ma Long zai yi karawa da takwarorinsu na ketare domin samun lambobin zinariya.
Kamar yadda Ma Long yake, 'yar wasa Liao Yali ta lardin Hunan ta yi suna ne ko da yake tana da shekaru 19 da haihuwa. Kafin taron wasanni na birane na kasar a karo na 6, Liao Yali ta taba samun nasarori da yawa. A wannan karo kuwa ta sake nuna kyakkyawar gwanintarta, ta zama zakara a cikin gasar ninkaya ta rigingine mai tsawon mita 200 cikin sauki. Bayan samun lambar zinariya, ta ce,'Na gamsu da abin da na yi a cikin gasar. A kwanan baya, ban sami horo bisa shirin da aka tsara ba, amma duk da haka na saki jikina a lokacin da nake iyo.'
Liao ta ci gaba da cewa, za ta inganta aikin horo bisa halin da take ciki a nan gaba, za ta yi kokari domin samun maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic na Beijing.
1 2 3
|