Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-13 16:56:13    
Gine-ginen musulunci na jihar Ningxia

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da saduwa da ku a wannan fili na "Musulmai na jihar Ningxia a ganin Kande". Ni ce Kande ke jan akalar shirin. Daga ran 4 ga wata zuwa ran 4 ga wata mai zuwa wato Disamba, ina yin intabiyu a jihar Ningxia ta kasar Sin, shi ya sa mun tsara wannan shiri na musamman wato "Musulmi na jihar Ningxia a ganin Kande" domin gabatar muku musulmai na jihar Ningxia da kuma zamansu. To, a cikin shirinmu na yau, zan yi muku wani bayani kan gine-ginen musulunci na jihar Ningxia.

Jihar Ningxia ta kabilar Hui ta kasar Sin da aka kafa ta a shekara ta 1958 tana gabashin yankunan da ke arewa maso yammancin kasar Sin, fadinta ya kai murabba'in kilomita dubu 66.4, yawan mutanenta ya kai miliyan 6, a ciki yawan 'yan kabilar Hui wadanda suke bin addinin Musulunci ya zarce miliyan 2, shi ya sa jihar Ningxia jiha ce mafi girma wajen samun musulmai a duk fadin kasar Sin.

Lokacin da muke isa wurin shan iska na al'adun musulmi da ke gundumar Yongning ta birnin Yinchuan, hedkwatar jihar Ningxia, na saurari wannan waka. Ko da yake ban fahimci abin da ke cikin wakar sosai, amma ya jawo hankalina sosai domin dadin jinsa.

An gina wannan wurin shan iska ne da ke da halin musamman na musulunci bisa tallafawar musulmai da ke nuna kauna ga al'adun musulunci da kuma gwamnatoci na matakai daban daban na kasar Sin, haka kuma shi wuri daya tak a kasar wajen nuna al'adun gargajiya na kabilar Hui.

Bayan da muka shiga babbar kofa, sai mun ga wani dakin nuna kayayyakin tarihi na kabilar Hui da ke cibiyar wannan wurin shan iska, inda ake iya ganin kayayyakin tarihi masu dimbin yawa da aka nuna wajen tarihin kabilar Hui ta kasar Sin, da yunkurin shimfida wayin kai na musulunci, da al'adun gargajiya na kabilar Hui, da babbar gudummowar da kabilar Hui ta bayar a tarihin kasar Sin, da kuma bunkasuwar kabilar Hui ta jihar Ningxia. Wata mai ja-gorarmu ta gaya mana cewa, kakanin kakanin musulmai na kasar Sin sun zo kasar ne ta hanyar siliki wadda aka shimfida a daular Han ta yamma wato a shekara ta 119 kafin haihuwar Annabi Isa. "Hanyar siliki muhimmiyar hanya ce wadda wayewar kai ta kasar Sin a zamanin da ta yadu zuwa kasashen yamma. Kuma gada ce mai hade da tattalin arziki da al'adu na kasar Sin da kasashen yamma. Kuma kakanin kakanin musulmai na kasar Sin wato Larabawa sun zo kasar Sin ne ta hanyar domin yin cinikayya, haka kuma a daidai sabo da haka, addinin musulunci ya shigo kasar Sin."

1 2