
Hei Guifang, wata 'yar kabilar Hui ce da ta zo daga gundumar Tongxin da ke kudancin jihar Ningxia wadda ke fama da talauci sosai, ta shiga makarantar a shekarar nan da muke ciki, kuma ta gaya mana cewa, idan ba ta samu wannan zarafi mai kyau wajen yin karatu a wannan makaranta ba, to ba yadda zai yi sai dole ne ta je sauran wurare domin cin rani. A cikin babbar makarantar dutsen Liupan, ana iya samun'yan makaranta kamar Hei Guifang masu dimbin yawa, kashi 40 cikin dari daga cikinsu 'yan kabilar Hui ne, kuma kashi 80 cikin dari daga cikinsu sun zo ne daga yankunan karkara.

Wani jami'in ofishin kula da aikin koyarwa na jihar Ningxia yana ganin cewa, idan ana iya ba da tabbaci ga ko wane yaro na yankunan da ke kan duwatsu wajen samun ilmi, to za a canja zaman rayuwansu, haka kuma iyalansu za su samu alheri sosai.(Kande) 1 2
|