Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-09 15:39:04    
Jihar Ningxia ta kasar Sin

cri

Daga ranar 5 ga watan da muke ciki zuwa ranar 5 ga wata mai zuwa, wakiliyarmu Kande za ta shafe tsawon wata guda tana ziyara a jihar Ningxia ta kasar Sin, domin yin ziyarar bude ido tare kuma da kawo wa masu sauraronmu labaran da ke shafar jihar nan. Kafin Kande ta kama ziyara gadan gadan, mun gabatar da wani bincike a kan ra'ayoyin masu sauraronmu game da wannan ziyarar Kande, kuma a kwanan baya, mun sami amsoshi daga wajensu.

Malam Salisu Dawanau, mai sauraronmu da ya zo daga birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, "Hakika, ziyarar da Malama Kande za ta kai Jihar Ningxia ziyara ce wadda za ta bai wa dukkan masu saurarenku damar sanin wannan jiha mai tattare da ni'imtattun wurare masu ban mamaki da sha'awa.Wannan irin ziyara abu ne mai kyau musamman saboda ita kanta Malama Kande za ta kara iliminta na sanin wannan jiha da kuma fadakar da sauran mutane. Saboda haka, ina ganin mu masu saurarenku za mu so sanin irin yanayin rayuwar mutanen Jihar Ningxia, da irin nasu gudunmuwar wajen daukaka al'adunsu da kuma yadda su kan yi marhaban ga baki masu kai musu ziyara ta musamman. Bayan haka, na san kuma masu saurarenku za su so sanin wuraren zuba jari da kuma hanyoyin da mutum zai bi wajen harkokin kasuwanci da yawon bude ido da dai sauransu. Sai mun sake ji daga gare ku yayin da kuka fara gabatar da wannan shiri."

Sai kuma malam Mamane Ada daga birnin Yamai, jamhuriyar Nijer, wanda ya rubuto mana wasikar da ke cewa, abun da nike so bisa wannan ziyarar bude ido ta malama kande shi ne, a yi kokarin ba mu bayani kan matsayin wannan jihar a kan sauran jihohin kasar Sin, sa'an nan a ba mu cikakken bayani bisa kabilun wannan jihar, a game da baki masu zuwa can yaya suke dubin bako wajensu, daga karshe wane abun kida suka fi amnfani da shi cikin galgajiyarsu.

Sa'an nan, akwai kuma malam Bala Mohammed Mando, mazaunin birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, "Na yi farin cikin samun wannan sakonku a kan ziyarar da Kande za ta yi a jihar Ningxia. Ina fatan za a ba mu cikakken tarihin muhimman wurare da kuma muhimman mutanen wannan jiha. A bayanna mana wuraren yawon bude ido da ke wannan jiha domin yin ziyara da masana'antun da za su iya hadin gwiwa da na kasashenmu, domin samo hanyoyin sadarwa da hadin kai a tsakanin jihar Ningxia da jihohin Afirka. Sa'an nan, a bayyana mana al'adu da sana'o'i da addinai da kuma wasannin shakatawa na jama'ar wannan jiha da ci gaban wannan jiha wajen fasaha da kimiyya da kuma kere-kere tare kuma da hanyoyin noma da yadda jama'ar jihar suke samar wa kansu abinci. Sa'an nan, tambayoyina su ne, shin mene ne matsayin jihar Ningxia a tarihi da siyasa da al'adu da kuma cigaban kasar Sin, wane rawa wannan jiha take takawa a wajen tattalin arzikin kasar Sin, musamman a fannin kere-kere. Wadanne abubuwa ne kasashe masu tasowa irin Nijeriya za su iya koya daga wannan jiha ta fannin noma da tattalin arziki da kuma cigaban jama'arsu.

1 2