Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-07 17:50:13    
Wasan kwallon kwando na kasar Sin ya sami ci gaba tare da NBA

cri

A shekarar 2004,an taba shirya gasar kasar Sin ta farko ta kawancen NBA a birnin Shanghai na kasar Sin,kawo yanzu,shekaru uku da suka wuce,gasar `preseason` wato zango na farko na shekarar gasa ta NBA ta sake zuwa birnin Shanghai wato garin Yao Ming,shahararren `dan wasan kwallon kwando na kasar Sin.Yanzu kungiyar `Cleveland Cavaliers` da kungiyar `Orlando Magic` sun sake zuwa kasar Sin domin shiga gasa,ana ganin cewa,kawancen NBA yana kara habaka kasuwarsa a kasar Sin.

A cikin wadannan kungiyoyi biyu wadanda aka kafa su ba da dadewa ba,kungiyar `Cavaliers` ta riga ta shiga babbar gasa ta karshe ta NBA a cikin shekarar gasa da ta gabata,`yan wasa taurari mafiya yin suna a duniya dake cikinsu Lebron James da Dwight Howard su ma suna nuna mana babban karfinsu.Yanzu dai,ba ma kawai ana mai da hankali kan nune-nune masu ban sha`awa na `yan wasan NBA ba,har ma ana kara ba da muhimmanci kan ribar kasuwancin da gasar ta kawo mana.A ran 17 ga watan Oktoba,bayan da aka kammala gasar zango na farko na shekarar gasa ta NBA tsakanin kungiyar `Cavaliers` da kungiyar `Magic`,bi da bi ne babban manajan NBA David Stern,da direktan cibiyar kula da harkar wasan kwallon kwando ta kasar Sin Li Yuanwei suka yi sharhi kan hadin gwiwar kasuwanci tsakanin NBA da kungiyar wasan kwallon Kwando ta kasar Sin.A cikin shirinmu na yau,bari mu kawo muku bayani kan wannan.

A halin yanzu,ana iya cewa,wasan kwallon kwando ya riga ya shiga kasuwa sosai da sosai,wato yana kawo mana riba mai tsoka,`yan wasa taurari da gasanni masu ban al`ajabi suna kara karuwa a kwana a tashi.David Stern ya bayyana cewa,dalilin da ya sa kungiyoyin NBA dake karkashin jagorancinsa suke zuwa kasar Sin bi da bi shi ne domin neman samun ribar kasuwanci.Yanzu a kasar Sin,NBA ta riga ta kafa ofishinta a birnin Beijing da birnin Shanghai da kuma yankin musamman na Hongkong.Nan gaba kuma NBA za ta kara tsara shirin bunkasuwarta a kasar Sin bisa mataki daban daban kuma daga duk fannoni.Stern ya ce,  `Bisa mataki na farko,za mu gina filin wasan kwallon kwando a wurare daban daban na kasar Sin;na biyu,za mu kafa ajin horo ga `yan wasa da malaman koyarwa mafiya nagarta,haka kuma za mu daga matsayin kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin;na uku,za mu yi hadin gwiwa da CBA wato hadaddiyar gasar sana`a ta wasan kwallon kwando ta kasar Sin,ta yadda za a kago NBA na kasar Sin.Wadannan su ne shirye-shirye na dogon lokaci,da fatan mu nuna kwazo da himma mu yi kokari tare.`

1 2