Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-29 14:46:35    
Ya kamata mu nace ga hanyoyin zaman gurguzu mai sigar musamman Sin kuma mu inganta tsarin babban taron wakilan jama'a

cri
Ran 28 ga wata, memban zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Mr Wu Bangguo ya jaddada cewa, kamata ya yi mu cusa akidar babban taro na 17 na jam'iyyar kwaminis ta Sin cikin kwakwalwarmu, kuma mu gudanar da dukkan ayyuka bisa akidar nan. Haka kuma mu nace ga hanyoyin zaman gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, kuma ya kamata mu tsaya tsayin daka kan tsarin babban taron wakilan jama'a da kuma inganta shi.

Mr Wu Bangguo ya bayyana haka a gun taro na 30 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a a karo na 10. Aiwatar da akidar babban taro na 17 shi ne babban manufar siyasa da ke gaban kome a yanzu kuma aiki ne da ya kamata a gudanar a tsawon lokaci na nan gaba. Tsarin babban taron wakilan jama'a shi ne babban tsarin siyasa ta kasar Sin, haka kuma shi ne tsarin dimukuradiyya na jama'a da ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Ya kamata mu dage kan yin amfanin da tsarin ra'ayin zaman gurguzu mai sigar musamman a Sin wajen jagorancin gudanar da ayyukan babban taron wakilan jama'a, ta yadda shari'ar da babban taron wakilan jama'a ya zartas da kuma kuduran da ya yanke za su bayyana ra'ayoyin jam'iyyar kwamnis ta Sin, kuma za su dace da halin Sin da babbar moriyar mutane, da kuma ingiza dukan ayyukan babban taro zuwa sabon matsayi.(Bako)