Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-29 14:20:56    
Tafkin Qinghai wurin zama ne ga bil adama da tsuntsaye gaba daya

cri

Malam He Yubang, mataimakin shugaban hukumar kula da yankin da ake bayar da kariya ga yanayin kasa na tafkin Qinghai ya bayyana wa wakilan gidan rediyonmu cewa, "idan wani yana so ya bar wani abinsa a tsibirin, to, zai bar sawun kafarsa, idan wani ya tashi da wani abu, to, zai tashi da hotonsa. A tsibirin nan na Tsuntsaye, babu dakin cin abinci da hotel da dakin nishadi da kuma sauran gine-gine, sai ya kasance da ni'imataccen yanayin kasa. "

Yayin da wakilanmu suka hau kan dakalin kallon tsuntsaye da ke a bakin tafkin a karkashin jagorancin Malam He, sai suka yi farin ciki da ganin tsuntsaye iri daban daban wadanda ke tashi a sararin sama, ko yin iyo a cikin tafkin, ko kuma yin hutawa a kan duwatsun tafkin yadda suka ga dama, kukan da tsuntsaye ke yi na da dadin ji kwarai.

Tafkin 'Qinghai' mai fadin muraba'in kilomita 4,300 tafkin ruwan gishiri ne mafi girma a kasar Sin, kuma nan ne fadamu mai muhimmanci sosai. Bayan da lardin Qinghai ya mayar da tsibirin tsuntsayen da ya zama yankin da ake bayar da kariya ga yanayin kasar a shekarar 1975, sai ta aika da 'yan gadi zuwa tsibirin don kiyaye muhallinsa. Bayan haka, an sha fadada fadin yankin. Ya zuwa shekarar 1997, duk girman yankin nan ya wuce kadada dubu 495.


1 2 3 4