Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-24 17:31:47    
Shan taba a waje zai iya yin illa ga lafiyar dan Adam

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan taba a waje zai yi illa ga lafiyar dan Adam, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan taron baje koli na karo na goma na kimiyya da fasaha na birnin Beijing na kasar Sin.

Mutane masu yawa suna ganin cewa, shan taba a waje ba zai yi illa ga lafiyar sauran mutane ba, a hakika dai wannan ba daidai ba ne. Bisa wani nazarin da jami'ar Stanford ta kasar Amurka ta yi a kwanan nan, an ce, hayakin da masu shan taba suka busa shi ma zai iya yin illa ga lafiyar sauran mutanen da suka shaki hayakin tabar ba tare da son rai ba.

Manazarta sun gudanar da wani bincike kan tasirin da shan taba ke yi a gefen tituna, da dakunan cin abinci da ke gefen titi, da tashoshin bos-bos, da kuma jami'o'i. Daga baya kuma sakamakon bincike ya gano cewa, ko da a waje, hayakin da masu shan taba suka busa zai iya gurbata iskar da ke kewayensu, sabo da haka sauran mutane za su sha wahala sakamakon shakar gurbatacciyar iska.

Mataimakin furofesa Neill a fannin ayyukan kiyaye muhalli na jami'ar Stanford da ya sa hannu a cikin binciken ya bayyana cewa, shakar hayakin taba a gida ko a waje dukkansu za su iya yin illa ga lafiyar jiki, kuma idan wani mutum ya yi kusa kusa da masu shan taba, to illar da hayakin taba zai yi masa za ta fi tsanani. Sinadari mai guba da ke cikin taba zai iya yin illa ga zuciya da kuma tsarin numfashi na dan Adam, haka kuma zai tsananta cutar tarin asthma.

Ban da wannan kuma rahoton ya nuna cewa, a ko wace shekara, dubban 'yan kasar Amurka ne ke mutuwa sakamakon cututtukan da shakar hayakin taba ke haddasawa. Shi ya sa lokacin da ake mai da hankali a kan magance shakar hayakin taba a gida, ya kamata a dora muhimmanci kan illar da shakar hayakin taba a waje ke bayarwa.

Tun da shan taba yana illa sosai ga lafiyar dan Adam, shi ya sa masu shan taba da yawa suke neman yin watsi da shan taba, amma da kyar suke iya samun nasara. Masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suna ganin cewa, mai yiyuwa ne wannan yana da nasaba da wasu kwayoyin halitta wato Gene na jikin dan Adam.

Bisa labarin da mujallar ilmin kwayoyin hali ta bayar, an ce, wata kungiyar bincike ta kasar Amurka ta gudanar da wani bincike ga mutanen da suka samu nasara wajen yin watsi da shan taba da kuma wadanda suka fadi a kan wannan batu wajen kwatanta kwayoyin halitta nasu. Daga baya kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, dalilin da ya sanya da matukar kyar wasu mutane ke iya yin watsi da shan taba shi ne sabo da kwayoyin halitta nasu.

Dr. George Ure da ya sa hannu a cikin nazarin kwayoyin halitta ya ce, kwayoyin halitta 221 na mutanen da suka samu nasarar yin watsi da shan taba da kuma na wadanda suka fadi yin haka sun sha bamban. Kuma kwayoyin halitta a kalla 62 da ke sanya nicotine ya zama jiki ga masu shan taba.

Wani manazarci na jami'ar Duke ta kasar Amurka ya bayyana cewa, ana fatan za a iya tabbatar shirye-shiryan jiyya mafi amfani bisa salon kwayoyin hallita iri daban daban na masu shan taba.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan taron baje koli na karo na goma na kimiyya da fasaha na birnin Beijing na kasar Sin.