Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 20:18:58    
Zaben sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na JKS sun nuna burin duk 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jama'ar Sin

cri
Ran 23 ga wata, jaridar People's Daily za ta ba da bayanin edita mai lakabi haka 'an sami ingantacciyar kwayar jagorancin sha'anin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin', inda aka bayyana cewa, sakamakon zaben sabbin shugabannin hukumomin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya nuna tunanin duk jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma burin dukkan al'ummar kabilun kasar Sin.

Bayanin ya bayyana cewa, an zabi sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a gun cikakken zama na farko da kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na karo na 17, inda Hu Jintao ya sake zama babban sakataren kwamitin tsakiya, sa'an nan kuma, yawan kusoshi masu ilmi da kyawawan halaye wadanda suka fi karancin shekaru sun shiga kwamitin tsakiya da kuma hukumomin shugabanci na kwamitin tsakiya na sabon karo. Wannan ya shaida cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta sami kyakkyawan ci gaba, 'yan jam'iyyar sun fi karancin shekaru, haka kuma suna da karfi da kwarewa.

Ban da wannan kuma, bayanin ya kara da cewa, kirar babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 da kuma cikakken zama na farko na kwamitin tsakiya na karo na 17 na jam'iyyar sun tabbatar da manufar da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma jama'ar Sin suke bi domin samun bunkasuwa, haka kuma, sun aza muhimmin harsashin tunani da siyasa ga jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ta ci gaba da jagorancin al'ummar kabilun kasar Sin domin yin hadin gwiwa da gwagwarmaya, sa'an nan kuma, sun samar da ingantaccen tabbaci wajen kula da harkokin jami'ai.(Tasallah)