Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-22 14:12:22    
Kafofin watsa labari a ketare sun mai da hankali sosai kan rufewar babban taro na JKS na 17

cri

A ran 21 ga wata a birnin Beijing, aka rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 cikin nasara. Wasu manyan kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun bayar da labaran rufewar taron cikin lokaci, haka kuma sun mai da hankali sosai kan sabon kwamitin tsakiya da aka zaba, da sabon kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a, da kudurin gyararren shirin kundin mulki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da aka zartas da shi.

Kamfanonin watsa labaru na 'Jiji News Agency' da 'Kyodo News Agency' na kasar Japan suna ganin cewa, shigar da ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya cikin kundin mulki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya bayyana matsayin kasar Sin na mai da hankali sosai kan zaman rayuwar jama'a, kasar Sin za ta kokarta wajen kafa zaman al'umma mai jituwa a nan gaba, ta yadda za ta samu bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin dogon lokaci, da rage gibin kudin shiga da jama'ar Sin ke samu, da kare muhalli, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.

Kamfanin watsa labaru na 'Yonhap News Agency' na kasar Korea ta kudu ya bayyana cewa, shigar da ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya cikin kundin mulki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin zai zama wata muhimmiyar ishara a tarihin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

Kamfanonin watsa labaru na 'Associated Press' na kasar Amurka da Reuter da 'Agence France Presse' na kasar Faransa sun bayar da labarai game da sabon kwamitin tsakiya da aka zaba, da sabon kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a, da kuma nasarar rufewar taron. Reuter yana ganin cewa, nufin tafiyar da ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya shi ne, domin manoma da ma'aikata za su kara samun fa'idar bunkasuwar tattalin arizki, da kuma kyautata halin da ake ciki dangane da gurbacewar iska da ruwa.

Kamfanin watsa labaru na kasar Jamus shi ma ya bayar da labarai game da rufewar babban taro na 17, da shigar da ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya cikin kundin mulki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, inda ya bayyana cewa, ra'ayin samun bunkasuwa ta kimiyya ya bukaci kasar Sin ta tsaya kan samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, da kyautata bunkasuwar tattalin arizki maras daidaici, da kafa zaman al'umma mai jituwa.(Danladi)