Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 22:03:17    
Kasar Sin ta gama muhimman ayyukan share fagen wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing

cri

Mataimakin shugaban birnin Beijing, kuma mataimakin shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing, Mr. Liu Jingmin ya bayyana a ran 19 ga wata a birnin Beijing cewa, an rigaya an gama muhimman ayyukan share fage na lokaci daban daban ga wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing bisa shirin da aka tsara, wannan dai ya aza tubali mai inganci ga yin wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing cikin nasara.

Mr. Liu Jingmin ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya gana da manema labaru a ran nan a cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin. Ya ce, ban da aikin gina filin wasan motsa jiki na kasar Sin da za a kammala a watan Maris a shekara mai zuwa, za a kammala aikin gina filayen wasan motsa jiki guda 37 da za a yi amfani da su a lokacin wasannin Olympic kafin karshen shekarar nan, an riga an tabbatar da shirin bikin bude wasannin Olympic da bikin rufe wasannin Olympic na Beijing, ana yin aikin nan, kuma ana yin aiki da kyau wajen yin odar sayen tikitoci da kuma sayar da su. Bugu da kari, yawan mutane masu aikin sa kai na wasannin Olympic ya karu, yawan mutanen da suka yi rajista ya zarce dubu 670.

Ban da haka kuma, ana fara aikin share fagen wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008, an rigaya an tabbatar da aikin gina gine-gine marasa shinge na kowane filin wasan motsa jiki.(Asabe)