Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-19 16:28:42    
Kasar Sin ta sami sakamako mai kyau yayin da take kokarin cika alkawarinta shirya wasannin Olympic bisa akidar kiyaye muhalli

cri
Ran 19 ga wata, mataimakin magajin birnin Beijing kuma mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr Liu Jianming ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin tana kokarin cika alkawarinta kan shirya wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 bisa akidar kiyaye muhalli, kuma ya zuwa yanzu, ta sami sakamako mai kyau.

Mr Liu Jianmin ya bayyana haka a gun taron manema labaru a cibiyar yada labaru ta babban taron 17 ta jam'iyya kwamnis ta kasar Sin. Ya bayyana cewa, a cikin ayyukan shirya wasannin Olympic, kasar Sin tana himmantuwa wajen gudanar da manufar shirya wasannin Olympic bisa akidar kiyaye muhalli, ala misali, yayin da kasar sin take fasalta dakuna da filaye, tana gudanar da ayyuka bisa ra'ayin kiyaye muhalli, kuma su kan yi amfani da kayan gine-gine marasa illa ga muhali, hakazalika kuma masana'antu da suka tallafa wa shirya wasannin Olympic ba su keta shari'ar kiyaye muhali ba, ya kamata masana'antun da za su samar da abinci da abin sha yayin wasannin Olympic su yi amfani da abubuwan kiyaye muhali. Dadin daddawa kuma, shirya wasannin Olympic ya sami babban ci gaba wajen sha'anin ciyar da kiyayen muhallin birnin Beijing gaba, ta hanyar yi amfani da makamashin da za a iya sake yin amfani da shi, da kuma rage yawan abubuwan masu gurbata muhalli, ingancin muhallin halittu na birnin Beijing ya sami kyautatuwa, yawan kwanakin da ake da ingancin iska mai kyau a shekarar 2006 ya kai kashi 66 cikin kashi dari da ke cikin duk shekara, ya karu da kashi 18 cikin kashi dari idan an kwatanta da makamacin lokaci na shekarar 2000, yawan wurare da suke lallube da tsire-tsire ya kai kashi 42 cikin kashi dari.(Bako)