Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 22:00:42    
Ba za a canja hanyar da ake bi wajen yin gyare-gyaren tsarin tsaida darajar kudin Sin RMB ba

cri
Shugaban bankin tsakiya na kasar Sin, wato bankin jama'ar kasar Sin Zhou Xiaochuan ya bayyana yau 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ba za a canja hanyar da ake bi wajen yin gyare-gyaren tsarin tsaida darajar kudin Sin wato RMB ba.

Mr. Zhou ya fadi cewa, kasar Sin za ta daukaka cigaban aikin yin gyare-gyaren tsarin tsaida darajar kudin Sin RMB, ba za ta canja hanyar da ake bi wajen sanya yawan kudin Sin dake samarwa da bukatu cikin kasuwanni ya kara taka muhimmiyar rawa yayin da ake tsaida darajar kudin Sin RMB ba, a sa'i daya kuma, ba za ta canja hanyar da take bi wajen yunkurin cimma manufar canja kudin Sin RMB zuwa kudaden musanya yadda aka ga dama ba.

Dangane da sanarwar da ministocin kudi na kasashe 13 na shiyyoyin da ake yin amfani da kudin Euro suka bayar a kwanan baya, inda suka maida hankulansu kan matsayin darajar kudin Sin RMB, Zhou Xiaochuan ya bayyana ra'ayinsa cewa, karuwar rarar kudin da kasar Sin ta samu wajen yin cinikayya tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai shi ne babban dalilin da ya haddasa wannan lamari. Jami'an bankin tsakiya na kasar Sin za su yi musanyar ra'ayoyi da shawarwari tare da bangaren kungiyar tarayyar Turai kan batun darajar kudin Sin RMB, yayin da ake gudanar da taron shekara-shekara na bankin duniya da asusun bada lamuni na kasa da kasa.(Murtala)