Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 19:06:37    
Zancen wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin a kan raya zaman al'umma mai jituwa

cri
A gun wani muhimmin taron da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kira a shekarar 2004, a karo na farko ne jam'iyyar ta gabatar da akidar "raya zaman al'umma mai jituwa". Yau shekaru uku ke nan da aka gabatar da akidar, kuma "raya zaman al'umma mai jituwa" ya riga ta zama wani muhimmin nauyin da ke bisa wuyan gwamnatin kasar Sin. A gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na karo na 17 da ake yi a yanzu a nan birnin Beijing, raya zaman al'umma mai jituwa shi ma ya zama daya daga cikin abubuwan da ke jawo hankulan wakilan da suka zo daga wurare daban daban.

Mr.Zhao Yuzhong, wakili ne da ya fito daga birnin Chaohu na lardin Anhui na kasar Sin, kuma shi wani lauya ne da ke cikin cibiyar ba da taimakon shari'a da ke wurin. A nan kasar Sin, cibiyar ba da taimakon shari'a hukumar musamman ce da ke gudanar da aikin ba da taimakon shari'a da kuma taimakawa marasa galihu a madadin gwamnati. Mr.Zhao Yuzhong ya bayyana cewa,"wannan hukumar ba da taimakon shari'a tamu ta kafu ne a shekarar 1996, a lokacin, kudade kalilan ne muka samu daga gwamnati, amma yanzu suna da yawa, me ya sa? Sabo da gwamnati ta kara mai da hankalinta a kan batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'a, kuma da yawa daga cikin batutuwan zaman rayuwar jama'a suna shafar batun adalci, idan an daidaita batun, to, za mu iya kara samun jituwar zaman al'umma."

Batun adalci da Mr.Zhao Yuzhong ya ambata a baya wani kashi ne na aikin raya zaman al'umma mai jituwa da Sin ke yi. Bayan da Sin ta fara aiwatar da manufar gyare-gyare da kuma bude kofa ga kasashen waje, bisa saurin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da masana'antu da kuma garuruwa, sabani iri iri sun kara tasowa. Alal misali, rashin daidaicin bunkasuwa a tsakanin birane da kauyuka da kuma yankuna daban daban, da matsalar samun aikin yi da rashin cigaban aikin ba da ilmi a kauyuka da dai sauransu. Daidai sakamakon irin halin da ake ciki ne, Sin ta gabatar da akidar raya zaman al'umam mai jituwa, don fuskantar matsalolin kamar yadda ya kamata.

Mr.Xu Guangguo, wani wakili a gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na 17, kuma sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke birnin Mudanjiang na lardin Heilongjiang na kasar Sin, ya yi nuni da cewa, abin da ya fi rashin samun jituwa a birnin Mudanjiang shi ne rashin daidaici tsakanin yankuna daban daban a fannin bunkasuwar tattalin arziki. Gundumar Suifenhe da ke cikin birnin tana makwabtaka da gundumar Muling. Kasancewar gundumar Suifenhe wata tashar da ke budewa ga kasar Rasha, tattalin arzikinta tana kan gaba, a yayin da gundumar Muling ta kasance gundumar da ke rashin samun ci gaba a fannin tattalin arziki. Don taimakawa gundumar, gwamnatin birnin Mudanjiang ta yanke shawarar bunkasa masana'antun kere-keren kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje a gundumar Muling, wato bisa fifikon da gundumar Suifenhe ke da shi, kuma an cimma kyawawan nasarori, Mr.Xu Guangguo ya ce,"da ma gundumar Muling gunduma ce da ke dogara bisa aikin noma, amma a cikin 'yan shekarun nan, masana'antunta sun bunkasa cikin sauri, wadanda kuma suka dogara musamman bisa kayayyakin da ake shigowa daga kasashen waje, wannan ya sa kaimi sosai ga bunkasuwar masana'antunta, haka kuma ya sa kaimi ga samar da guraben aikin yi da kuma kudin shiga na gwamnati, kai har ma da tattalin arzikin wurin."

Ma iya cewa, samun aikin yi babban tushe ne ga zaman rayuwar jama'a. Arewa maso gabashin kasar Sin da ma yanki ne da aka samu dimbin kamfanonin mallakar gwamnati, kuma a lokacin da tattalin arzikin kasar Sin ya sauya zuwa irin na kasuwanci, kamfanonin da yawa sun lalace, kuma batun samun aikin yi ya taba zama wata matsala mai tsanani a shiyyar, amma yanzu, halin ya canza. Mr.Zhang Jiehui, wani wakili a gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta Sin da ke birnin Anshan da ke arewa maso gabashin kasar Sin ya ce,"a cikin shekaru da dama, muna dukufa a kan daidaita batun samar da aikin yi, yanzu mun rage iyalan da ke fama da matsalar da yawansu ya kai 13,635. Ya zuwa yanzu dai, matsalar ta sassauce."(Lubabatu)