Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-18 14:31:37    
Kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin wadda za ta shiga taron wasannin Olympic na Beijing za ta kunshi 'yan wasa kimanin 570

cri

A ran 17 ga wata, shugaban babbar hukumar motsa jiki ta kasar Sin Mr. Liu Peng ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin wadda za ta shiga taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 za ta kunshe da 'yan wasa kimanin 570, kuma za ta zama kungiyar wakilan 'yan wasa mafi girma da ke shiga taron wasannin Olympic a tarihin kasar Sin.

Ya furta cewa, ya zuwa karshen watan Satumba na shekarar da muke ciki, kasar Sin ta rigaya tana da 'yan wasa kimanin 500 da suka samu damar shiga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing. Yanzu kuma, wadansu wasannin neman shiga taron wasannin Olympic ba su gamawa ba, an kiyasta cewa, akwai sauran 'yan wasa kimanin 70 za su iya samun damar shiga taron wasannin Olympic na Beijing. Sabo da haka, kungiyar wakilan 'yan wasa ta kasar Sin wadda za ta shiga taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing tana kunshe da 'yan wasa kimanin 570. (Zubairu)