Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-17 18:12:07    
Shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da dama sun dudduba rahoton babban taron wakilan JKS a karo na 17 tare da wakilan taron

cri

Jiya 16 ga wata, an cigaba da gudanar da babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 a nan birnin Beijing. Manyan shugabannin kasar Sin, ciki har da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao suka yi tattaunawa tare da wasu kungiyoyin wakilai, inda suka dudduba rahoton da aka bayar a gun babban taron wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 tare da wakilan taron.

Ran nan, shugaba Hu ya yi tattaunawa tare da kungiyar wakilai ta lardin Jiangsu. Bayan da ya saurari jawabai da wakilan suka bayar a tsanake, shugaba Hu shi ma ya bayar da jawabinsa a matsayin wani wakilin tawagar Jiangsu kan yadda za a nakalci da fahimci wannan rahoto. Ya fadi cewa, wannan rahoto yana cike da hikima da hazikanci na duk jam'iyyar kwaminis ta Sin da daukacin mutane 'yan kabilu daban daban na duk kasa. Bayan da aka yi masa gyare-gyare da kuma tattauna a kansa, to, labuddah wannan rahoto zai zama wata sanarwar siyasa kuma ka'idar ayyuka wadda za a aiwatar da su domin cigaba da raya sha'anin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a cikin sabon tarihi.

Bugu da kari, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wen Jiabao ya yi tattaunawa tare da kungiyar wakilai ta lardin Sichuan, inda ya hakkake cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen bin hanyar raya sha'anin gurguzu mai sigar musamma na kasar Sin, da nacewa ga bin manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen ketare, da tabbatar da akidar samun cigaba ta hanyar kimiyya, da kuma sa kaimi ga raya wata zamantakewar al'umma mai jituwa.

Dadin dadawa, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Jia Qinglin ya shiga tattaunawa tare da kungiyar wakilai ta birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a zurfafa aikin tabbatar da akidar samun cigaba ta hanyar kimiyya, da sanyawa bangarori daban daban sabon kuzari, da kara karfinsu na kirkira cikin himma da kwazo, ta yadda za a tattara hazikanci da karfi daga duk fadin kasar Sin wajen gina zamantakewar al'umma mai wadata.

Yayin da zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Wu Guanzheng ke hira tare da kungiyar wakilai ta jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta, ya tabo magana ta musamman kan batun yakar almubazzaranci. Yana mai cewa, dangane da magance wannan matsala, ya kamata a yanke hukunci da yin rigakafi tare, da dora muhimmanci sosai kan aikin yin rigakafi, da inganta aikin yaki da cin hanci da rashawa da nuna abubuwa masu da'a.(Murtala)