Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-16 14:20:24    
Masu sauraronmu na ketare suna mai da hankulansu kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin

cri

Yayin da ake yin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin na 17, masu sauraronmu suna taya murnar bude taron ta hanyoyi dabam daban.

Mai sauraronmu da ya fito daga Nijeriya Salisu Dawanau ya aiko mana wasikar Email cewa, cikin rahoton da Hu Jintao ya bayar, ya waiwayi kokarin da JKS ta yi da sakamokon da ta samu wajen kara karfin kasa da wadata kasar. Ya jadadda muhimmanci na bunkasa kasa cikin lumana da shimfida zaman lafiya da dinkuwar kasa daya da kuma yin gyare-gyare cikin JKS kanta. Daukacin abubuwan da Mr Hu ya ce sun yi daidai da ayyukan da gwamnatin Sin ta yi cikin idanun masu sauraronmu. Mai sauraro Mamane Ada ya nuna cewa, rahoton Hu Jintao ya shafi abubuwa da dama kuma wajen fannoni da yawa, inda akwai tarin abubuwa mafi jawo hankulan masu sauraron da suka fito daga Afrika.

Mai sauraro na Kenya Joyce Mhavile ya aiko mana wasikar Email cewa, ta saurari labarin budewar babban taron ta gidan rediyon kasar Sin dake Nairobi, rahoton Hu Jintao ya jawo hankalinta sosai. A ganinta, ya kamata, kasashen Afrika su koyi goguwar da kasar Sin ta samu wajen gina kasa.(Lami)