Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-16 10:48:25    
Rahoton da babban sakatare Hu Jintao ya yi ya nuna ka'idojin jagoranci a cewar manyan shugabannin J.K.S.

cri

Ran 15 ga wata da safe, an bude babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17 a nan birnin Beijing, babban sakatare Hu Jintao na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya wakilci kwamitin tsakiya na jam'iyyar na 16 ya gabatar da wani rahoto. A wannan rana da yamma, yayin da Mr. Wu Bangguo memban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya da sauran manyan shugabanni na J.K.S. suka yi shawarwari sun nuna babban yabo ga wannan rahoto.

Mr. Wu Bangguo ya ce, wannan rahoto ya ba da amsa ga manyan tamboyoyi na J.K.S. yayin da take ciki wannan muhimmin lokacin yin kwaskwarima da raya kasa, wato irin tutar da J.K.S. za ta daga, da hanyar da J.K.S. za ta bi, da ra'ayin da za ta yi, da kuma manufar da za ta bi don ci gaba da samun bunkasuwa. Ya kara da cewa, wannan rahoto shi ne wani rahoto mai ka'idojin jagoranci da ke dacewa da zamani, kuma zai sa kaimi ga sha'anin raya kasa.

Mr. Zeng Qinghong, memban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na J.K.S. ya ce, rahoton babban taron muhimmiyar takardar tsare-tsaren ka'idoji ne da ke nuna matsayin fahimtar J.K.S wajen ka'idojin rike da ragamar mulkin kasa, da ka'idojin raya zaman al'umma ta gurguzu, da kuma ka'idojoin bunkasuwar zaman takewar 'yan Adam.