Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 15:30:55    
Ma'aikata ta farko ta samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da tsire-tsire a kasar Sin

cri

Gunduma mai suna "Shan" ta Lardin Shandong babban wurin noman auduga ne a kasar Sin. A karshen shekarar bara, a gundumar nan, an kafa ma'aikata ta farko ta samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da tsire-tsire a kasar Sin. Ba ma kawai ma'aikatar ta taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin wurin ba, har ma ta ba da taimako wajen tsimin makamashi da kiyaye muhalli.

Tsire-tsire makamashi ne mafi girma na hudu a duniya bayan kwal da man fetur da kuma gas. Tsire-tsiren da ake amfani da su wajen samar da wutar lantarki sun hada da karan shinkafa da auduga da masara da dawa da dagwalon itatuwa da kuma sauransu. Sabo da makamashin da ake samu daga wajen tsire-tsiren makamashi ne mai tsabta kuma ba tare da gurbata muhalli ba, shi ya sa gwamnatin kasar Sin tana ba da kwarin guiwa sosai ga bunkasa irin wannan makamashi, kuma ta dauki aikin yin amfani da makamashin tsire-tsaire bisa matsayin babbar manufar samun bunkasuwar makamashi mai dorewa.

Malam Zhou Tingying, shugaban ofishin kula da harkokin makamashi na hukumar aikin noma ta gundumar Shan ya bayyana cewa, gundumarsa wata babbar gunduma ce a fannin aikin noma da na gandun daji. Manoman gundumar suna noman alkama da auduga da gyara da makamantansu a filayen gona masu fadi sosai, sabo da haka muna iya samun karan tsire-tsare da dagwalon itatuwa masu dimbin yawa don samar da wutar lantarki. Ya kara da cewa, "yawan manoman gundumar Shan ya kai dubu 970, fadin gonakinta kuma ya kai kadada dubu 100, haka kuma fadin gonakin da ake noman auduga ya wuce kadada dubu 20, lalle, tsire-tsiren da muke samu don samar da wutar lantarki sun yi yawan gaske.


1 2