Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 13:58:51    
Kamata ya yi Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta bi ka'idar raya kasa ta hanyar kimiyya,in ji Hu Jintao

cri

Yau ran 15 ga watan Oktoba ,a makwafin kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin,sakatare-janar na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Hu Jintao ya bayar da wani rahoto ga wakilai mahalarta taro na 17 na Jam'iyyar,rahoton da ya bayar dake da lakabin haka "A yi kokarin samun sabbin nasarori wajen raya kasa daga dukan fannoni a karkashin tutar zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin."

Rahoton ya kasu gidaje 12. Muhimman abubuwan dake cikin rahoton su ne waiwayen ci gaban da aka samu a cikin shekaru biyar da suka gabata da takaitaccen bayani kan tarihin yin gyare gyare da bude kofa na tsawon shekaru talatin, da bayanai kan abubuwan da aka tanada a cikin manufar raya kasa ta hanyar kimiyya da muhimmiyar ma'ana da take da ita ga ci gaban kasar Sin da shirye shiryen ayyukan da aka tsara domin nan gaba wajen tattalin arziki da siyasa da al'adu da zamantakewa da tsaron kasa da kuma harkokin waje da haduwar kasa gu daya da sauransu a kasar Sin.

A cikin rahotonsa da farko Hu Jintao ya takaita nasarorin da mutanen kasar Sin suka samu a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta Sin tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka yi kafin shekaru biyar.Ya ce "shekarun biyar da suka gabata, shekarun ne da kasar Sin ta samu babban cigaba wajen kawo sauyi da bude kofa da shimfida zamantakewa mai dadi daga dukkan fannoni.ainihin tattalin arzikin kasa ya kara karfi,zaman rayuwar mutanen kasa na kara kyautatuwa,mutanen da suka samu aikin yi sun kara yawa,an kara inganta tsarin samar da tabbaci ga zaman mutanen kasa,da kara inganta tsarin samar da kiwon lafiya ga kowa da kowa da ba da hidima wajen ayyukan jinya,da tabbatar da samar da ilimi ba tare da biyan kudi ba a makarantun kauyuka."

A cikin rahotonsa,Hu Jintao ya gabatar da ka'idar raya kasa ta hanyar kimiyya da ya kamata Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta bi kwata kwata. Ya kuma yi bayani filla filla kan abubuwan da aka tanada a cikin wannan akida da kumma yadda aka fitar da ita. Ya ce abu mafi muhimmanci a cikin akidar raya kasa ta hanyar kimiyya shi ne raya kasa da ba da fiffiko ga mutane,muhimmin bukatu kuma su ne a samu daidaituwar ci gaba mai dorewa a dukkan fannoni, kuma muhimmiyar hanyar da ya kamata a bi ita ce kula da cigaba a birane da karkara,da ci gaba a yankunan daban daban,da cigaban tattalin arziki da na zamatakewa,da ci gaban bil Adam da kyautatuwar muhalli,a kula da cigaba a gida da harkokin bude kofa ga kasashen waje.Ya bukaci Jam'iyyar kwaminis ta Sin da ta tabbatar da akidar raya kasa ta hanyar kimiyya a duk fagage na harkokin tattalin arziki da na zamantakewa kwata kwata.


1 2