Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 12:05:45    
An soma babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 17

cri

A ran 15 ga wata, jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar Sin, wato jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta soma babban taron wakilanta na duk kasar a karo na 17 a babban dakin taro na jama'a na Beijing. Muhimman jami'ai na jam'iyyar da wakilan da aka gayyace su da su halarci wannan babban taro musamman da wakilai fiye da 2200 da aka zabe su daga dukkan 'yan jam'iyyar fiye da miliyan 70 ta hanyar dimokuradiyya sun halarci wannan babban taro tare.

Mr. Wu Bangguo, memban zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shugabanci bikin kaddamar da wannan babban taro yau. Bisa shawarar da ya bayar, dukkan wakilai sun nun juyayi har na tsawon minti 1 ga marigaya shugabannin jam'iyyar da na kasar Sin, ciki har da Mao Zedong, da Deng Xiaoping, da sauran jarumai wadanda suka rasu lokacin da suke neman 'yancin kasar Sin. Sannan babban sakatare Hu Jintao na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya wakilci kwamitin tsakiya na jam'iyyar na 16 ya gabatar da wani rahoto da ke da lakabi haka "A daga tutar gurguzu da ke bayyana halin musamman na kasar Sin sama domin cigaba da yin kokarin neman samun sabuwar nasara wajen raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi".

Rahoton da Hu Jintao ya gabatar ya kunshi batutuwa 12, wato batun ayyukan da jam'iyyar ta yi a cikin shekaru 5 da suka wuce da batun nazari kan fasahohin da jam'iyyar ta samu a cikin shekaru kusan 30 da suka wuce bayan da ta soma aiwatar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A waje daya kuma, Hu Jintao ya bayyana tunanin neman bunkasuwa ta hanyar kimiyya da muhimmiyar rawa da wannan tunani zai taka wajen bunkasuwar kasar Sin. Bugu da kari kuma, Hu Jintao ya  bayar da shirye-shiryen neman cigaba a fannonin tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'umma da tsaron kan kasar da harkokin diplomasiyya da hadin kan kasar Sin gaba daya da ciyar da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin gaba. (Sanusi Chen)