Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-15 08:24:06    
An kira taro na karo na farko na kungiyar shugabancin babban taron wakilan JKS na 17

cri

A ran 14 ga wata da yamma a birnin Beijing, an kira taro na karo na farko na kungiyar shugabancin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17, inda aka zartas da zaunannun kwamitin na kungiyar da ke kunshe da membobi 36, ciki har da Hu Jintao da rahoton dudduba wakilan da za su halarci wannan babban taro da ajandar babban taron. A waje daya, a gun taron, an tabbatar da cewa za a soma babban taron a ran 15 ga wata, kuma za a rufe shi a ran 21 ga watan da muke ciki.

A cikin rahoton dudduba wakilan da za su halarci babban taron da kwamitin dudduba wakilai na babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gabatar, an ce, an zabi wakilai ne bisa Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ajandar da kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya shirya. Yawan wakilan da ya kamata su halarci babban taron zai kai 2213. Wadannan wakilai suna dacewa da sharudan da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya tsara gaba daya, su nagartattun 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne. Yawancin jama'a suna amincewa da su, kuma sun samu fifiko a cikin aikin da suke yi. A waje daya, suna da karfin tattaunawa kan lamura iri iri, kuma suna wakiltar bangarori daban-daban.

Wannan rahoto ya kuma bayyana cewa, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gayyaci wakilan musamman 57 da su halarci wannan babban taron wakilan jam'iyyar na karo na 17. Wadannan wakilan musamman suna da iko daya da na sauran wakilai. (Sanusi Chen)