Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-14 17:37:13    
An gama aikin share fagen babban taron wakilan jam'iyyar JKS na karo na 17 gaba daya

cri

A ran 15 ga wata, wato Litinin ne za a soma babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 a nan birnin Beijing. A ran 14 ga wata da yamma, kakakin wannan babban taro Li Dongsheng ya shirya wani taron manema labaru, inda ya bayyana cewa, za a yi wannan taro ne tun daga ran 15 zuwa ran 21 ga watan da muke ciki. Ya zuwa yanzu, an riga an gama dukkan ayyukan share fagen wannan babban taro.

An labarta cewa, yawan wakilai wadanda za su halarci wannan babban taro na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na karo na 17 zai kai 2213 wadanda suke wakiltar 'yan jam'iyyar miliyan fiye da 70. A waje daya, mr. Li Dongsheng ya ce, an riga an tabbatar da ajandar babban taron, wato za a saurari da dudduba rahoton da kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauraro da dudduba rahoton da kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar za su gabatar. A waje daya, za a dudduba da zartas da shirin yin gyare-gyare kan Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da zabar kwamitin tsakiya na 17 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da zabar kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar. (Sanusi Chen)