Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-12 20:53:16    
Sabunta: Za a soma babban taron wakilan JKS na karo na 17 a ran 15 ga wata

cri
A gun cikakken zama na 7 na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an tsai da kudurin cewa, za a soma babban taron wakilan jam'iyyar na karo na 17 a ran 15 ga watan da muke ciki.

An kira wannan cikakken zama na karo na 7 na kwamitin tsakiya na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne tun daga ran 9 zuwa ran 12 ga wata. A gun taron, an saurari da tattauna kan rahoton aiki da Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi a madadin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar. Haka kuma an tattauna da zartas da rahoton da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 16 zai gabatar wa babban taron wakilan jam'iyyar na karo na 17 da shirin kwaskwarima kan "Daftarin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin", kuma an tsai da kudurin cewa, za a gabatar da wadannan rahotanni 2 zuwa ga babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 17 domin dudduba su.

A waje daya, a gun taron, an yaba wa ayyukan da hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi bayan cikakken zama na 6 na jam'iyyar. An kuma yi sharhi kan ayyukan da aka yi bayan babban taron wakilan jam'iyyar na karo na 16. Kazalika, an bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu karfafuwa sosai, an kuma samu babban cigaba fannonin bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare. Ingancin zaman rayuwar farar hula ma ya samu kyautatuwa a bayyane. Haka kuma, an ci gaba kwarai wajen shimfida dimokuradiyya da dokoki. A waje daya, an bude sabon shafi wajen raya al'adu. An kuma soma ayyukan raya zaman al'ummomin kasar Sin. Ayyukan tsaron kasa da kokarin kyautata ingancin rundunar sojan kasar Sin sun kuma samu cigaba mai ma'anar tarihi. A sa'i daya, yankunan Hongkong da Macao sun samu kwanciyar hankali da bunkasuwa. An kuma kara mai da hankali kan ayyukan da suke da nasaba da lardin Taiwan. Kokarin aiwatar da harkokin diplomasiyya daga dukkan fannoni ya kuma samu muhimmin cigaba.

Bugu da kari kuma, an duba da zartas da rahoton bincike kan Chen Liangyu, tsohon memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma sakataren kwamitin Shanghai na jam'iyyar da Du Shicheng, tsohon sakataren kwamitin birnin Qingdao na lardin Shandong da kwamitin da'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gabatar, inda aka tabbatar da kudurin korar su daga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta zartas a shekarar da muke ciki. (Sanusi Chen)