Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 18:49:58    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(04/10-10/10)

cri
Ran 2 ga wata, a birnin Shanghai na kasar Sin, an bude taron wasannin Olympic na musamman na lokacin zafi na kasa da kasa a karo na 12. Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci bikin bude taron, inda ya kuma sanar da bude wannan muhimmin taron wasannin Olympic na musamman. Taron wasannin Olympic na musamman na kasa da kasa kasaitaccen taron wasannin motsa jiki ne da aka shirya domin nakasassu a kwakwalwa na duk duniya. Ana gudanar da wannan taron wasannin motsa jiki a Shanghai har tsawon kwanaki 10. An kuma samar da manyan gasanni 21 da kuma gasanni 4 ba domin samun lambar zinariya ba a wannan karo. 'Yan wasan Olympic na musamman da malaman horas da wasanni fiye da dubu 10 daga kasashe da yankuna 160 ko fiye sun shiga wannan taron wasannin motsa jiki a shekarar da muke ciki.

Ran 8 ga wata, a cibiyar wasan kwallon tennis da ke wurin yawon shakatawa na Olympic na Beijing, an bude gasar wasan kwallon tennis ta karba karba ta duniya ta GoodLuck Beijing da hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tennis ta kasa da kasa ta shirya, inda 'yan wasa 100 daga kasashe da yankuna 13 suke karawa da juna domin zama zakara. Za a rufe gasar a ran 20 ga wata.

Ran 7 ga wata, an rufe gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur a tsakanin kungiya-kungiya ta shekarar 2007 a birnin Magdeburg na kasar Jamus. A cikin karon karshe da aka yi, kungiyoyin kasar Sin maza da mata sun lashe kungiyar Hong Kong na kasar Sin maza da kungiyar kasar Korea ta Kudu mata bi da bi da cin 3 da ba ko daya, ta haka, dukkansu sun zama zakaru.

Ran 7 ga wata, budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Japan ta kawo karshe. A cikin karon karshe da aka yi a tsakanin mata biyu biyu, 'yan wasa Sun Tiantian da Yan Zi na kasar Sin sun zama zakaru bayan da suka lashe 'yar wasa Zhuang Jiarong ta Taipei ta kasar Sin da 'yar wasa Vania King ta kasar Amurka da ci 2 da 1.

Ran 7 ga wata, an kammala budaddiyar gasar wasan kwallon badminton ta Macao ta kasar Sin a shekarar 2007. A cikin karon karshe da aka yi a tsakanin namiji da namiji a wannan rana, dan wasa Chen Jin na kasar Sin ya lashe shahararren dan wasa Taufik Hadayat na kasar Indonesia da ci 2 da 1, ta haka ya zama zakara. Sa'an nan kuma, 'yan wasan Sin sun sami lambobin zinariya a cikin gasa ta tsakanin mace da mace da ta tsakanin mata biyu biyu da kuma gasa ta gaurayawar namiji da mace a wannan karo.(Tasallah)