Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 17:17:23    
Wani babban malamin da ke da fasahar yin zane-zane kan kayayyakin fasahar hannu mai suna Zhang Tonglu

cri

Bayan da ya koma ma'aikatar, sai ya zama mai kula da harkokin ma'aikatar, ya yi kokarin koyon fasahar kera Jintailan cikin shekaru uku, sa'anan kuma ya kware wajen yin amfani da dukkan fasahohin kera Jintailan. Ya ce, da wuya sosai za a iya kwarewa wajen yin amfani da fasahar kera Jintailan, mutum daya ya iya kwarewa a wani fanni daya na kera shi kawai, tun daga daular Ming da daular Qing har zuwa yanzu, wato a cikin shekaru fiye da 600, kusan ba wanda aka same shi da ya iya dukkan fasahohin kera Jintailan ba . Amma bayan da na zama mataimakin shugaban ma'aikatar, na kware sosai wajen aikin kera Jintailan, na koyi dukkan fasahohin kera Jintailan, kuma na kafa tushena wajen kera Jintailan a wannan lokaci.

Amma abin bakin ciki gare mu shi ne, ma'aikatarsa ta karye bisa sakamakon saurin bunkasuwar zamantakewar al'umma da masana'antu na zamani.

Amma Zhang Tonglu bai rasa kokari ba, ya tattara tsofaffin abokan ma'aikatarsa ya kafa wani kamfanin kera kayayyakin fasaha a birnin Beijing, ya ce ya kamata a raya Jingtailan , kuma a lokacin kera Jintaila, ya yi gwaje-gwaje har sau dubu goma, a karshe dai ya fitar da kayayyakinsa zuwa kasashen waje,inda suka sami karbuwa sosai.

Zhang Tonglu ya yi tsammanin wallafa wani littafin da ke kunshe da fasahohin da ya samu wajen kera Jintailan cikin dogon lokaci, ya bayyana cewa, Wannan ne hakkina kuma nauyi da ke bisa wuyana,a da tofaffi masu kera Jintailan ba su taba rubuta kome a kan fasahar Jintailan ba ko kadan, don kiyaye abubuwan tarihi ba kayayyaki ba na kasar Sin, kamata ya yi mu yi kokarin rubuce-rubuce a kan fasahar da aka samu wajen kera Jingtailan domin zuri'armu.(Halima)


1 2