Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 15:19:16    
Manema labaru na gida da waje sun yi rajista domin taron JKS

cri

Tun daga aka fara yin aiki a cibiyar watsa labaru ta babban taro na 17 na wakilan kasa na jam'iyyar kwaminis ta Sin a ran 8 ga wata, yawan manema labaru na kasashen waje da suka yi rajista ya kara karuwa. Yanzu, yawan manema labaru suka yi rajista ya kai 1092, a cikinsu yawan manema labaru na kasashen waje ya kai 744.

Mataimakin darekta na cibiyar watsa labaru Mr. Zhu Shouchen ya bayyana cewa, a bayyane ne, yawan manema labaru na kasashen waje ya karu har ma ya wuce na babban taro na 16 na wakilan kasa na JKS wato 590. Muhimman kafofin watsa labaru na kasa da kasa, da na yankuna sun aika da manema labarunsu don watsa labaru na babban taro na 17 na wakilan kasa na JKS. Ban da haka kuma, manema labarun da suka yi rajista sun zo daga kasashe daban-daban dake wakiltar duk kafofin watsa labaru na nahiyoyin duniya 5.

Bugu da kari, Mr. Zhu Shouchen ya bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta bunkasa tattalin arzikin kasar kuma ta daga matsayinta a duniya, wadannan abubuwa ne suka jawo hankulan kafofin watsa labaru na kasa da kasa. Wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa yawan manema labaru na kasashen waje ya yi yawa.(Asabe)