Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-10 15:17:55    
Jam'iyya mai mulkin kasar Sin na himmantuwa wajen nazarin harkokin waje dake da sigar musamman

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, Jam'iyya mai mulkin kasar Sin wato Jam'iyyar Kwaminis ta Sin za ta kira wani sabo kuma babban taron wakilan duk kasa a tsakiyar wannan wata, inda za ta yi waiwayen fasahohin da ta samu wajen gudanar da harkokin mulkin kasar cikin shekaru biyar da suka gabata da kuma tabbatar da wassu muhimman manufofi da ka'idoji da jam'iyyar da kuma gwamnatin kasar za su aiwatar da su a nan gaba. 'A ran 18 ga watan jiya, ministan kula da harkokin cudanya da ketare na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Wang Jiarui ya gabatar da wani jami'in Jam'iyyar Demokuradiyya ta kasar Czech ga wassu jama'ar kasar Sin, wadanda suka yi farin ciki da samun damar kai ziyara a wannan muhimmin wuri'.

A yayin da take bude kofa ga jama'ar kasar, jam'iyyar kwaminis ta Sin tana kuma bude kofa ga jam'iyyun siyasa iri daban-daban na kasashen duniya, wadanda suka hada da jam'iyyun siyasa masu sassaucin ra'ayi, da jam'iyyun siyasa na al'umma da demokuradiyya, da jam'iyyun zamantakewar al'umma, da jam'iyyun aiki da kuma jam'iyyun siyasa masu tsattsuran ra'ayi da matsakaitan ra'ayi da dai sauransu. Mataimakin minista mai kula da cudanya da ketare na Jam'iyyar kwaminis ta Sin Mr. Liu Hongcai ya fada wa wakilinmu cewa : ' Rike mulkin kai cikin bugun gaba a hannu, da yin zaman daidai wa daida, da nuna girmamawa da juna da kuma rashin tsoma baki cikin harkokin gida da juna', Ka'idoji hudu ne da jam'iyyarmu take aiwatarwa game da harkokin waje. Yanzu, Jam'iyyar Kwaminis ta Sin tana yin cudanya da mu'amala tare da jam'iyyun siyasa da kungiyoyi da yawansu ya zarce 400 na kasashe da yankuna sama da 160'.

Bisa kididdigar da aka yi an ce, cikin shekaru biyar da suka shige, yawan tawagogin jam'iyyun siyasa na ketare wadanda jam'iyyar kwaminis ta Sin ta bada goron gayyatarzu zuwan nan kasar Sin domin yin ziyara ya wuce 1,000. Ban da wannan kuma jam'iyyar ta kulla sabuwar dangantaka tsakaninta da jam'iyyun siyasa kusan 30 na kasashe sama da 30.

Jama'a masu sauraro, manyan shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin suna mai da hankalinsu sosai kan yin mu'amala tare da jam'iyyun siyasa na ketare. Alkaluman da aka bayar na nuna cewa, tun bayan babban taron wakilan duk kasa na 16 na jam'iyyar kwaminis ta Sin, wasu shugabanni dake sama da matsayin mukamin wakilan ofishin siyasa na jam'iyyar har sau 50 ne suka ja ragamar kungiyoyin wakilai zuwa ketare domin yin ziyara.

A cikin musanye-musanye da jam'iyyar take yi tare da jam'iyyun siyasa na ketare, tana iyakacin kokarin samun sabbin aminai yayin da take tunawa da tsoffin aminai a ko yaushe. Mr. Liu Hongcai ya kara da cewa : ' Mu kan yi shawarwari kan bakin zaren bunkasa huldodin tsakanin kasa da kasa da musanya fasahohin gudanar da harokin mulkin kasa da kuma manufofin wadatar da kasa.'

Da yake kasar Sin tana kara samun karfin da take da shi na raya kasa daga dukkan fannoni da kuma daga matsayinta a kasashen duniya, shi ya sa kasashe da dama na duniyar suke begen kasar Sin za ta bada hannunta ga warware muhimman maganganun da suka janyo hankulan kasashen duniya. Lallai Jam'iyyar kwaminis ta Sin na kokarin cimma burinsu a fannin yin kwaskwarimar Majalisar Dinkin Duniya, da tinkarar sauyin yanayi na duk duniya da daukaka yunkurin shimfida zaman jituwa a fadin duk duniya haka kuma a akan batun nukiliyar Zarin Korea, da shawarwarin zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya da kuam batun halin da ake ciki yanzu a Palasdinu da Isra'ila da dai sauran fannoni. ( Sani )