Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-10-02 14:55:01    
An kara dora muhimmanci kan al'adun gargajiya na kasar Sin

cri

Tare da cigaban tattalin arzikin kasar Sin cikin shekarun baya, an kara dora muhimmanci kan al'adun gargajiya na kasar Sin.Wasan Kongfu wanda kusan kowa ya sani a duniya ya samu bunkasuwa domin matasa da yawa suna kishin wannan wasan..

Makarantar koyar da wasan Kongfu ta kasar Sin ta shimfidu ne a karkarar birnin Laizhou na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.Mista Li Mingzhi,shahararren dan wasan Kongfu a kasar Sin ya kafa ta a shekara ta 1992 bayan da ya koma mahaifarsa da ya yi watsi da aiki a kasashen waje da samun albashi mai tsoka.

Ga shi a yau makarantar nan ta samu babban cigaba cikin shekaru 12 da suka shige,makarantar nan ta horar da 'yan wasan Kongfu sama da dubu uku domin manyan makarantu da kungiyoyin wasanni da sauran sassan kasa,daga cikin 'yan wasa 75 sun zama zakara a duk kasa da 'yan wasan 32 sun zama zakara na duniya,makarantar nan tana daya daga cikin shahararrun makarantu 10 na koyar da wasan Kongfu a kasar Sin.Shugaban makarantar nan Mista Li Mingzhi ya gaya wa wakilinmu cewa " A wannan makaranta ba ma kawai ana koyar da wasannin Kongfu ba har ma ana koyar da ilmi ciki har da al'adu,idan masu koyon wasan Kongfu sun samu ilmi mai zurfi,za su iya kwarewa cikin wasannin da suke koyon da su zama nagartattun 'yan wasa.

Sabili da haka ake koyar da ilmin al'adu da na wasan Kongfu a wannan makaranta.An kasa abin da suke koyo zuwa sassa biyu,na farko ilmin al'adu kamar harshe da lissafi da dai sauransu na biyu kuwa wasan Kongfu.Dukkan ilmin da ake koyarwa a makarantun firamare da middle school ana koyar da su wannan makaranta,ban da wannan ana koyar da wasan Kongfu kamar wasan Karate da wasan Kongfu da aka bayyana cikin sinima.Duk 'yan makaranta suke zabar abin da suke so su koya.

Duk wanda ya shiga makarantar nan ya shiga ne bisa niyyarsa,yawancinsu suna kishin wasan Kongfu tun suna kanana,wani lokaci ma su kan yi fada a tsakaninsu in suna zama tare.Shi ya sa makarantar nan ta koya musu muhimmancin zaman lumana,da sun gane muhimmancin haka sai sun yi zama cikin jituwa.

Dan makarantar Zhi Yuntao,zakara ne na wasan makamancin dambe a kasar Sin a wannan shekara,wani abokinsa shi ma zakara ne na wannan wasa a lardin Shandong.Ga shi a yau su aminan juna ne.Amma a lokacin da suka shiga makaranta ba haka ya ke ba.sun taba yin fada.Mallamin koyarwa nasu Mista Liu Jiang ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa Bayan da wadannan 'yan makaranta guda biyu suka shiga makaranta,wata rana an yi wasan Kongfu,suka yi zage zage da juna saboda wani karamin abu,da mallamin koyarwarsu ya ga haka,ya taimaki kowanensu da ya gane kuskurensa,daga baya sun zama aminan juna.Su kan taimaki juna a cikin shekaru biyu na baya,har sun sami babbar nasara a cikin wasan.

Makarantar koyar da wasan Kongfu ta kasar Sin ta samu bunkasuwa,shugaban makarantar Mista Li Mingzhi yana nan yana tsara shirin makarantar a nan gaba yana so ya maida makarantar ta zama ta duniya.Ya ce Muna so mu maida makarantar koyar da wasan Kongfu ta zama ta duniya a kasar Sin kafin shekara ta 2008 ta yadda Karin baki za su samu fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin da wasan Kongfu da koyonsa.

A halin yanzu makarantar koyar da wasan Kongfu ta kasar Sin tana da sassa a jihar Califonia ta Amurka da birnin Paris na kasar Faransa,tana nan tana cikin shirin kafa wata sassa a birnin Seoul na Korea ta kudu.A halin yanzu da akwai daliban da suka zo daga Amurka da Canada da Italiya da Holland da Jamus da Isra'illa da Korea ta kudu da Japan suna koyon wasan Kongfu a wannan makaranta.Bisa alkaluman da aka bayar,an ce dalibai baki da suka yi karatu a wannan makaranta sun kai 160.