Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:42:53    
Karin bayani kan tunanin Mao Zedong

cri

Tunanin Mao zedong shi ne tsarin hasashen kimiyya da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda Mao Zedong ke shugabanta suka tsara bisa babban hasashen Marxanci da Leninnanci tare da takaita wadatattun fasahohin da aka samu a jere wajen juyin juya hali na kasar Sin cikin dogon lokaci da yin aikatawar hakika wajen raya kasa, wanda kuma ya dace da hakikanin halin da kasar Sin take ciki.

Tunanin Mao Zedong shi ne sakamakon da aka samu ta hanyar hada babban hasashe na Marxanci da Leninanci da aikatawa ta hakika wajen juyin juya hali na kasar Sin, kuma bunkasuwa ce da aka samu wajen yin amfani da Marxanci da Leninanci da raya shi a kasar Sin, sa'anan kuma takaitattun ka'idojin hasashe ne da fasahohi masu gaskiya dangane da juyin juya hali na kasar Sin, kuma an riga an tabbatar da su ta hanyar aikatawar hakika da aka yi, kuma shi ne sakamakon da aka samu ta hanyar yin amfani da hazikancin dukan rukunonin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Sharifci mai rai na tunanin Mao Zedong shi ne matsayi da ra'ayi da dabara da suka hada da sassa daban daban na juyin juya hali na kasar Sin da ayyukan raya kasa, suna da manyan fannoni uku, wato neman gaskiya daga abubuwan hakika da tafiyar da aiki ta hanyar jama'a da kuma neman 'yancin kai ba tare da tsangwama ba. Neman gaskiya daga abubuwan hakika shi ne abu mai muhimmanci da ke cikin tunanin Mao Zedong da kuma tushensa da mafarinsa, hakan kuma tafarki ne na tunanin Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Neman gaskiya daga abubuwan hakika shi ne a yi kome daga abubuwan hakika, kuma a hada hasashe da aikatawa gu daya, kuma a hada babban hasashe na Marxanci da Leninanci da aikatawar juyin juya hali na kasar Sin gu daya. Tafarkin jama'a shi ne a yi kome domin jama'a da kuma dogara bisa karfin jama'a. A fito daga jama'a kuma a koma wa jama'a. Neman 'yancin kai ba tare da tsangwama ba shi ne hasashen dole da aka bi wajen yin juyin juya hali da raya kasa ta hanyar hakikanin abubuwan kasar Sin da kuma dogara bisa karfin jama'a.

Mao Tsedong yana daya daga cikin masu kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an haife shi a shekarar 1893, kuma ya bar duniya a shekarar 1976, shi ne babban mutumin da ke cikin rukunin shugabanni na sabuwar kasar Sin na zuri'ar farko.(Fatima)