Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:42:25    
Dangantakar dake tsakanin jam'iyyar kwaminis ta Sin da kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin

cri

Kungiyar samari 'yan kwaminis ta kasar Sin wata kungiyar jama'a ce ta zamani dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ita ce makarantar da tarin samari ke koyon tsari na gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin da kwaminisanci ita kuma mataimakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma masu jiran kotakwana.

Farkon sunan kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin shi ne kungiyar samari 'yan gurguzu ta Sin. A watan Augusta na shekarar 1920, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta soma shirya kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin a birinin Shanghai. Sannan kuma a watan Mayu a shekarar 1922, kungiyar samari 'yan gurguzu ta Sin ta gudanar da taron majalisar wakilai na kasar na karo na farko a birnin Guangzhou bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin kai tsaye, inda ta kafa wata kungiya dake hade da kungiyoyin dake shimfide a duk kasar. A watan Janairu na shekarar 1925 a gun taron majalisar wakilan kasar na kungiyar a karo na uku, kungiyar nan ta yanke shawarar canja sunan kungiyar samari 'yan gurguzu zuwa kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin.

Kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin ita ce kungiyar jama'a da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kafa don hadin kai da samari da kuma koyar da su, ita ma wata gadar da ta hada jam'iyyar kwaminis ta Sin da samari. Kwamitin tsakiya na kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin yana karkashin jagoranci kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin. Kungiyoyin samari 'yan kwaminis ta Sin na matakai daban daban suna karkashin jagorancin kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin masu matsayi daya kuma a karkashin shugabannin kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin wadanda matsayinsu yake sama da su. Kamata ya yi kungiyoyin samari 'yan kwaminis ta Sin na matakai daban daban su aiwatar da ayyukansu da kansu bisa halayen da samari ke ciki da bukatunsu a karkashin shugabannin jam'iyyar.

A waje daya kuma, ya kamata kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na matakai daban daban su kara jagorancin kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin, kuma su mai da hakulansu wajen zaben shugabanni da horar da su. Kamata ya yi jam'iyyar kwaminis ta Sin ta nuna tsayayyen goyon baya ga kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin da ta aiwatar da ayyukanta bisa halayen musamman na samari da bukatunsu, kuma ta hanyar kagowa da kuma cikin rayayyen hali, su yi ayyuka da kyau wajen hada kan samari. Dukkan sakatarorin kwamitocin kungiyar samari 'yan kwaminis ta matakin gunduma ko kuma kasa da matakin gunduma, da sakatarorin kwamitocin kungiyar samari 'yan kwaminis ta Sin na sassan masana'antu da hukumomi, idan su 'yan jam'iyyar kwaminis ne za su iya halartar taron kwaminis na jam'iyyar kwaminis ta Sin mai matsayi daya da taron kwamitin din-din-din na majalisar wakilan.(Salamatu)