Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:41:02    
Tsarin yin hadin guiwa da shawarwari kan harkokin siyasa a tsakanin jam'iyyun siyasa daban daban da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin

cri

Tsarin siyasa da ake bi a kasar Sin ba ma kawai ya sha bamban da tsarin yin takara a tsakanin jam'iyyun siyasa biyu ko a tsakanin jam'iyyun siyasa da dama na kasashen yammacin duniya ba, har ma ya sha bamban da tsarin kasancewar jam'iyyar siyasa daya kadai a wasu kasashen duniya. A nan kasar Sin, ana bin tsarin yin hadin guiwa da shawarwari kan harkokin siyasa a tsakanin jam'iyyun siyasa daban daban da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. An tabbatar da kuma kafa wannan tsarin jam'iyyun siyasa a kasar Sin ne bayan da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da sauran jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya suka yi juyin juya hali da raya kasa da kuma yin gyare-gyare a kasar Sin a cikin shekaru da yawa da suka gabata. Sabo da haka, wannan tsari yana kasancewa a kasar Sin yanzu tamkar wani tsarin siyasa na tushe.

Halin musamman na wannan tsarin yin hadin guiwa da shawarwari a tsakanin jam'iyyun siyasa daban-daban da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne, jam'iyyun siyasa suna hada kan juna a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana rike da ragamar mulkin kasar Sin, sauran jam'iyyun siyasa suna halartar harkokin siyasa na kasar. A waje daya, jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna hada kan juna kuma suna halartar harkokin siyasa tare a matsayin jam'iyyun siyasa na abokantaka, amma ba jam'iyyun siyasa da ke adawa da juna ko jam'iyyun siyasa ne da ba su da ikon mulkin kasar ba. Jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya suna kuma shiga aikin tsarawa da aiwatar da manufofi da dokokin mulkin kasar. Halin da ake ciki a kasar Sin ya tabbatar da cewa, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin muhimmin sharadi da tushe ne ga tsarin hada kan jam'iyyun siyasa daban-daban da ake aiwatarwa a kasar Sin. Amma a waje daya, irin wannan jagoranci da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ke yi ba ya nufi cewa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana yin kome da kome ba, sai tana ba da jagoranci kan harkokin siyasa, ciki har da ka'idojin siyasa da makomar siyasa da muhimman manufofi da ka'idojin mulkin kasar.

Tsarin hada kan jam'iyyun siyasa daban-daban da tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa da ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba ma kawai suna hada da ra'ayoyin jam'iyyun siyasa na dimokuradiyya da kungiyoyin jama'a da nagartattun mutane da sa kaimi kan jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar da gwamnatocin matakai daban-daban da su tsai da kudurai bisa ilmin kimiyya ta hanyar dimokuradiyya ba, har ma suna daidaita moriyar jama'a na bangarori daban-daban. A waje daya, za a iya kaucewa zargin da mai yiyuwa ne za a yi sabo da jam'iyyar siyasa daya kadai take mulkin kasar idan ba a sa ido a kanta ba, kuma za a iya kaucewa tashin hankali kan harkokin siyasa da rashin kwanciyar hankalin zaman al'ummar kasar sakamakon cacar baka da aka yia tsakanin jam'iyyun siyasa da yawa. (Sanusi Chen)