Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:36:58    
Raya al'adu na zamani

cri

Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta gabatar da tsarin hasashen ' Wakiltar abubuwa na fannoni uku' a kan cewa wajibi ne jam'iyyar ta wakilci bukatun bunkasuwar karfin aikin kawo albarka na zamani na kasar Sin ; sa'nnan ta wakilci manufar ci gaba na al'adun ci gaba na kasar Sin ; dadin dadawa ta wakilci babbar moriyar tarin jama'ar kasar Sin. Daya daga cikin bukatun ' wakiltar abubuwan na fannoni uku' shi ne, ya kamata jam'iyyar ta wakilci manufar ci gaba na al'adun ci gaba na kasar Sin har kullum. Yanzu ana kokarin raya zamantakewar al'umma mai wadata daga dukkan fannoni a kasar Sin. Hakan ya zama tilas a sanya babban karfi wajen bunkasa al'adun gurguzu da raya wayewar kai na gurguzu.

Rahoton da Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gabatar a gun babban taron wakilai na 16 na jam'iyyar ya yi nuni da cewa, a kasar Sin ta zamanin yau, bunkasa al'adun zamani na nufin cewa bunkasa al'adun gurguzu irin na al'umma da kimiyya domin jama'a, wanda ke fuskantar yunkurin raya kasa ta zamani, da duniya da kuma makomar nan gaba. Bunkasa al'adun ci gaba na nufin cewa ya kamata a nace ga bauta wa jama'a da gurguzu da bin ka'idar ' Bar furanni dari su tohu da sauraran ra'ayoyi daga fannoni da yawa' ; Sa'annan a nace ga fadakar da kan jama'a da tsarin sanin-ka na kimiyya, da bada jagoranci ga mutane da ra'ayoyin bainal jama'a na gaskiya, da kyautata fuskar mutane da halin kirki, da sa kaimi ga mutane da kyawawan littattafan karatu ,da gwabza babban karfi wajen bunkasa al'adun ci gaba, da nuna goyon baya ga kyakkyawan al'adu da yin gyare-gyaren al'adu maras ci gaba da kuma yin dagiya da lalataccen al'adu.

Al'adun ci gaba na kasar Sin ta zamanin yau, kamata ya yi a bi muhimmin tafarki na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a matakin farko-farko na gurguzu, da kuma samar da karfin ingizawa na yunkurin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ; Sa'annan irin wannan al'adu kamata ya yi ya kasance al'adu ne, wanda yake iya yayata kyakkyawan halayyar al'ummar kasar da kuma bayyana aniya da tattara karfin da 'yan kabilu daban-daban na kasar ; Kazalika, ya kamata irin wannan al'adu ya yayata da kuma gaji dukkan abubuwan gargajiya na-gari na al'ummar kasar Sin ,wanda kuma yake da sigar musamman ta kasar yayin da yake shigo da duk irin sakamakon al'adu daga kasashen waje. ( Sani Wang )