Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-17 19:31:40    
Zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin

cri

Zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin yana nufi a hada manyan ka'idoji na zaman gurguzu na kimiyya da ainihin halin raya zaman gurguzu na kasar Sin.Daga cikinsu zaman gurguzu dokokinsa da ainihin halinsa sanin kowa da kowa ne,halayen musamman suna nufin manyan ka'idojin zaman gurguzu da kasar Sin ke bi a halin yanzu.

Tun lokacin da aka soma sauye sauye da bude kofa ga kasshen waje,Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta hada manyan ka'idojin Markisanci da ainihin hali na kasar Sin da kuma halayen musamman na zamanin da muke ciki gu daya,ta bincike daga dukkan fannoni da tattara bayanai ta hanyar kimiyya kan darasin da aka tsamo wajen raya zaman gurguzu na kasar Sin,da nasarori da hasara da sauran kasashen gurguzu suka samu,da ci gaba da koma baya da kasashe matasa suka samu wajen raya kasa,da ci gaba da sabane sabanen da ake samu a kasashe masu sukuni,ta amsa wasu muhimman tambayoyi a jere kan zaman gurguzu na kasar Sin dangane da hanyar raya kasa da matakin tarihi da manyan ayyuka da muhimmin shiri,tare da nasara ta bude wata hanyar raya zaman gurguzu mai halayen musamman.

Kan tattalin arziki,kasar Sin ta nace ga bin muhimmin tsarin tattalin arziki wanda a ciki aka dauki tsarin mallakar jama'a a matsayin ginshiki da tattalin arziki na tsarin mallaka daban daban na samu ci gaba tare da samo wani sabon yanayi wanda a ciki kungiyoyi masu bin tsarin mallaka daban daban su yi tserereniya kafada da kafada da samun ci gaba tare wajen bunkasa tattalin arziki.Kan harkokin siyasa,kasar Sin ta nace ga bin tsarin majalisar wakilan jama'ar kasa da tsarin hadin kan jam'iyyun siyasa da dama wanda Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ke jagora da yin shawarwari kan harkokin siyasa,da tsarin kula da kansu a yankunan da kanana kabilu ke zaune.A kan al'adu,ta nace ga daukar tsarin tunani na zaman gurguzu tamkar abin jagora ga zamantakewa,da neman samun ra'ayi daya bisa girmamawa banbancin dake kasancewa,da samo karin ra'ayi bai daya tare da sauran ra'ayoyin dake akwai.Ayyukan da aka yi sun tabbatar da cewa zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin wata hanya ce da ya wajaba a bi wajen mai da kasar Sin kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu mai wadata da dimakuradiya da wayin kai da jituwa,haka kuma hanyar nasara ce.(Ali)