Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-05 14:39:45    
Wace illa ce hauhawar farashin man fetur ya haifar ga kasashen Afirka?

cri

Cikin wani lokaci mai tsawo da ya wuce, kullum farashin gurbataccen man fetur ya rika hauhawa a kasuwannin kasashen duniya, wace illa ce hauhawar farashin man fetur ya haifar ga Afirka? Wannan matsala ta jawo hankulan kasashen duniya sosai. An ce ko da yake yanzu wannan matsala ba ta jawo illa ga Afirka a bayyane ba, amma kada a kasa kula da hadarin da ta haifar ga kasashen Afirka.

Cikin 'yan watannin nan da suka wuce, yawan gurbataccen man fetur da aka sayar bai ishi mutanen duniya ba, yawan bukatun da ake da su ya karu, halin siyasa da ake ciki a wasu kasashe masu arzikin mane futur ya yamutse, kuma an yi ta zuba jari da yawa domin hautsina maganar farashin man fetur, shi ya sa farashin man fetur ya kara tashi a kasuwannin kasashen duniya. A ran 31 ga watan Yuli, yawan farashin gurbataccen man fetur da ofishin kula da harkokin cinikin kayayyaki na birnin New York ya tsayar a watan Satumba na wannan shekara ya kai dalar Amurka 78.21 kan kowace ganga, wato ya wuce na matsayin koli na tarihin da aka kago a ran 14 ga watan Yuli na wannan shekara na dalar Amurka 77.03 kan kowace ganga.

Ba shakka, hauhawar farashin man fetur a kasuwannin kasashen duniya ta sa wasu kasashen Afirka da su yi abubuwan sadaukarwa da yawa domin shigo da man fetur, amma har zuwa yanzu, yawan illar da aka haifar ga kasashe masu shigo da man fetur sakamakon hauhawar farashin man fetur bai wuce tsammanin mutane ba.

Bari mu dauki kasar Kenya, kasa mafi girma wajen tattalin arziki ta gabashin Afirka a kama da masali, bisa matsayinta na kasa mai shigo da man fetur daga kasashen waje, yawan kudin da kasar Kenya ta kashe domin shigo da man fetur ya kai kashi 23 cikin 100 bisa jimlar kudaden da ta kashe wajen sayen kayayyaki daga kasashen waje. Bisa kididdigar da hukumar Kenya ta yi an ce, yawan karuwar tattalin arziki da kasar Kenya ta samu cikin watanni 3 na farkon wannan shekara ya kai kashi 6.3 bisa 100, wato ya wuce na makamancin lokaci na shekarar bara, a lokacin kuwa adadin nan ya kai kashi 4.1 bisa 100 kawai. Sa'an nan kuma yawan raguwar darajar kudin da Kenya ta samu cikin watanni 3 na farkon wannan shekara ya kai kashi 7.4 bisa 100, wato ya rugu sosai idan an kwatanda shi da na makamancin lokaci na shekarar bara, a wancan lokaci kuwa yawan adadin ya kai kashi 17.8 bisa 100.

1 2