Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-09-04 17:12:30    
Kasar Sin tana inganta ayyukan horar da likitoci na kananan hukumomi domin shawo kan cutar sukari

cri

Cutar sukari wata cuta ce da ba a iya warkar da ita kwata-kwata. Amma ta hanyar yin jiyya bisa kimiyya kamar yadda ya kamata, ana iya shawo kan tsanantar cutar. Sabo da haka, Abun na da muhimmancin gaske ga mutane da suka kamu da cutar sukari wajen tabbatar da cutar tun da wuri da kuma yin muwu jiyya ta hanyar kimiyya. Wu Mingjiang, mataimakin shugaban kungiyar ilmin likitanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Cutar sukari wata cuta ce da ake iya tabbatar da ita da kuma yi mata jiyya. Idan an ci gaba da kyautata kwarewar masu aikin likitanci wajen aiki domin suka iya tabbatar da cutar tun da wuri da kuma yin jiyya yadda ya kamata, to za a taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan cututtukan da cutar sukari ta haifar, da kuma rage yawan mutanen da suka mutu ko suka samu nakasa sakamakon cutar."

Tare da kyautatuwar zaman rayuwar Sinawa da kuma sauyawar salon zamansu, yawan Sinawa da suke fama da cutar sukari ya samu karuwa cikin sauri. A shekara ta 1979, yawan mutanen da suka fama da cutar ya kai kashi 0.67 cikin dari kawai, amma ya zuwa shekara ta 1996, wannan jimla ta kai kashi 3.6 cikin dari. Haka kuma a wasu wuraren kasar Sin, jimlar ta zarce kashi 5 cikin dari yanzu. Sabo da haka gwamnatin kasar Sin tana ta kara kebe kudade wajen taimaka wa asibitici da kuma hukumomin nazarin magunguna, ta yadda za a iya kara karfin shawo kan cutar sukari. Yanzu an fi samun albarkatun irin na ilmin figakafi da kuma shawo kan cutar a manyan biranen kasar Sin, amma da kyar likitoci da ke matsakaita da kananan birane musamman ma kauyukan kasar Sin suke iya samun damar sauraron laccar da kwararrun likitanci suka bayar, shi ya sa suka kasa fahimtar sabbin ilmi da fasahohi wajen warkar da cutar sukari.

A shekara ta 2004, ma'aikatar kiwon lafiya da kungiyar ilmin likitanci ta Kasar Sin sun shirya wani shiri wanda ake kiransa "sabuwar babbar ganuwa wajen kiwon lafiya" domin yin wa likitoci na kananan hukumomi furofaganda kan shawo kan cutar sukari. An aika da daruruwan kwararru zuwa asibitocin birane da kauyuka da ke larduna 23 na kasar Sin domin ba da kwasa-kwasan horaswa, da kuma yada sabbin fasahohi wajen yin jiyya ga masu fama da cutar sukari, ta yadda za a iya inganta kwarewar likitocin wuraren nan wajen tabbatar da cutar da kuma warkar da ta. Furofesa Chen Hong na asibitin Zhujiang na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin yana daya daga cikin kwararru a fannin shawo kan cutar sukari da aka aika da su a cikin harkar. Kuma ya gaya mana cewa, "Ta hanyar shiga cikin shirin, na gano cewa, likitoci na kananan hukumomi sun rasa ilmin shawo kan cutar sukari sosai, kuma ilmin da suka samu tsoho ne, sabo da haka an yi illa sosai wajen raya ayyukan shawo kan cutar sukari na kananan hukumomi."

1 2