Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-28 15:39:11    
Cin gishiri kadan yana iya shawo kan cututtukan zuciya da hauhawar jini

cri

Manazarta na kasar Amurka sun bayar da wani rahoto a kan mujallar ilmin likitanci ta kasar Birtaniya, cewa bayan da suka gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci, sun gano cewa, rage yawan gishirin da a kan ci zai iya rage yiyuwar kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini da kuma yiyuwar mutuwar mutane sakamakon wadannan cututtuka.

Wata kungiyar bincike da ke karkashin jagorancin Nancy Cook ta asibitin kula da lafiyar mata na Brigham na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Harvard ta kasar Amurka ta yi bayanin cewa, ta gudanar da wani bincike na dogon lokaci ga mutane 3126, wadanda bugun jininsu ya yi sama, kuma sun fi saukin kamuwa da cutar hauhawar jini.

A cikin wannan bincike na shekaru 10 zuwa 15, sabo da an rage yawan gishirin da wadannan mutane suka ci, shi ya sa yawan mutanen da suka kamu da cututtukan zuciya da hauhawar jini ta ragu da kashi 25 cikin dari. Kuma game da wadanda suka kamu da wadannan cututtuka, yawansu da suka mutu ya ragu da kashi 20 cikin dari.

Haka kuma kungiyar binciken ta nuna cewa, sabo da ta gudanar da wannan bincike ga mutane masu dimbin yawa cikin dogon lokaci, shi ya sa ta samu wata shaida mai karfi, wato lalle cin gishiri kadan zai iya rigakafin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini.

Ban da wannan kuma wani sabon nazarin da kasar Amurka ta yi ya bayyana cewa, cin abinci da yawa da ke da hatsi kadai zai iya rage hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka bayar, an ce, manazarta na jami'ar Wake Forest ta jihar North Carolina ta kasar Amurka sun samu wannan sakamako ne bayan da suka gudanar da wani bincike ga mutane wajen dubu 285 kan al'adar cin abinci da kuma lafiyar jikinsu.

Bisa ma'aunin da hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar Amurka ta bayar, an ce, abincin da ke da hatsi kadai shi ne abincin da ake yi da alkama da sha'ir da dai sauran hatsi, wanda yake kunshe da vitamin da fibre da trace elements da kuma sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant, ta haka zai ba da tasiri sosai wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu, da kuma shawo kan toshewar hanyoyin jini.

Haka kuma manazarta sun nuna cewa, ba kawai cin abinci da ke da hatsi kadai yana iya shawo kan cututtukan zuciya da hauhawar jini ba, har ma yana iya bayar da amfani wajen shawo kan cututtukan ciki da kuma cutar sukari.(Kande)