Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-27 15:36:41    
Wasu labarun jihohin Mongoliya ta gida mai cin gashin kansu ta kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko dai ga wasu labaru game da jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta.

Labarin farko shi ne an shirya bikin nune-nunen cigaban da aka samu a jihar Mongoliya ta gida a cikin shekaru 60 da suka wuce

A ran 5 ga wata, cikin hadin guiwa ne kwamitin jihar Mongoliya ta gida ta jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin da gwamnatin jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin sun shirya nune-nunen cigaban da aka samu a jihar cikin shekaru 60 da suka wuce a dakin nune-nune na jihar Mongoliya ta gida da ke birnin Hohhot, hedkwatar jihar.

Wannan biki na daya daga cikin bukukuwan murnar cikon shekaru 60 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin. An kasa wannan biki har kashi 8, wato kashin nune-nunen bunkasuwar jihar da kashin nune-nunen jituwar da ake samu a jihar da nune-nunen kyaun gani na Mongoliya ta gida da dai makamatansu.

Mr. Yang Jin, shugaban gwamnatin jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ya ce, tabbas ne jami'ai da jama'a na kabilu daban-daban na jihar za su kara fahimtar jihar ta wannan nune-nune. Kuma za su kara hada kansu domin kara ciyar da tattalin arziki da zaman al'umma na jihar gaba cikin hali mai kyau kuma cikin sauri tare da bayar da sabuwar gudummowarsu wajen shimfida jituwa da wadata da bunkasuwa a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta.

Wani labari daban shi ne an wallafa litattafai iri 80 domin murnar cikon shekaru 60 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta.

Kwanan baya, kamfanonin dab'i na jihar Mongoliya sun bayar da litattafai iri 80 domin murnar cikon shekaru 60 da kafuwar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A ran 6 ga wata, an yi bikin nunin wadannan litattafai a birnin Hohhot, hedkwatar jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta.

An labarta cewa, wadannan litattafai iri 80 suna kunshe da tsofaffin litattafan tarihi da adabi da hotuna da na yada ilmi da dai makamatansu. Suna bayyana cigaban da aka samu a fannin dab'in na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta hanyoyi daban-dabam. A waje daya, an rubuta ire-iren wadannan litattafai 28 cikin harshen Mongoliya.

An bayyana cewa, galibin taken wadannan litattafai suna yada kyawawan al'adun al'ummar kabilu daban-daban na jihar.

Labarin karshe shi ne an gano wani babban ma'adinan kwal a jihar Mongoliya ta gida.

Kwanan baya, hukumar kasa da albarkatu ta jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta bayar da labari cewa, an gano wani sabon ma'adinan kwal a jihar, inda aka adana kwal fiye da ton biliyan 5.

Hukumar kasa da albarkatu ta jihar Mongoliya ta gida ta bayyana cewa, kaurin wannan sabon ma'adinan kwal yana dacewa da yin amfani da injuna wajen hakar kwal.

Jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin jiha ce da take da yawan ma'adinan kwal mafi yawa a kasar Sin. Ya zuwa yanzu, yawan ma'adinan kwal da aka gano a jihar ya riga ya kai ton biliyan 650.(Sanusi Chen)