Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-14 15:14:36    
Gidan ibada na Confucius a birnin Nanjing na lardin Jiangsu

cri

A kudancin birnin Nanjing a lardin Jiangsu, a gabar kogin Qinhuaihe, an sami sabon yanki mai ci gaban tattalin arziki, inda akwai gine-gine da gidaje da shaguna da kuma dakunan cin abinci da aka gina su ta hanyar gargajiya irin na zamanin daular Qing na kasar Sin wato tsakanin shekarar 1636 da ta 1912. Shi ne kuma wani shahararren wurin yawon shakatawa.

Gidan ibada na Confucius yana nan cikin wannan yanki. Gidan ibadan nan ya ruguje a sakamakon hare-haren da 'yan hari Japanawa suka kai masa a shekarun 1940, amma an sake gina shi daga baya.

A farkon zamanin daular Ming wato tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1644, a kan shirya jarrabawar gama gari a wannan hedkwatar kasar Sin a lokacin can a ko wadanne shekaru 3. Duk cewar an mayar da birnin Beijing a matsayin sabuwar hedkwatar kasar Sin a shekarar 1421, mutanen da suka nemi zama jami'ai sun ci gaba da zuwa birnin Nanjing daga lardunan da ke kusa da Nanjing. A babban zauren jarrabawa, akwai kananan dakuna dubu 20 da dari 6, inda masu shiga jarrabawa suke shafe kwanaki 3 suna yin jarrabawa a tsanake. An rufe su a cikin wadannan kananan dakuna, haka kuma, an sa ido a gare su domin haramta yin magudi. An samar da abinci a ko wace rana, ta haka wadannan masu neman zama jami'ai sun iya jure wahalhalu na tsawon wadannan kwanaki 3.(Tasallah)