Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-07 17:42:50    
Ana sa ran alheri ga sake yin shawarwari a kan batun Darfur

cri

A ranar 6 ga wannan wata, a birnin Arusha da ke arewacin kasar Tanzaniya, an yi bikin rufewar taron kasashen duniya da Majalisar Dinkin duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afrika suka shirya cikin hadin guiwa. Bayan taron, Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afrika sun bayar da sanarwa cewa, rukunonin dakaru daban daban masu adawa da gwamnati da ke shiyyar Darfur kuma suke halartar taron sun riga sun tabbatar da cewa, za su yi shawarwarin karshe na shimfida zaman alfiya da gwamnatin Sudan cikin watanni uku masu zuwa. Ra'ayoyin jama'a suna ganin cewa, wannan ya bayyana cewa, ana sa ran alheri ga sake yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a kan batun Darfur.

Rukunoni masu adawa da gwamnati da ke shiyyar Darfur suna da yawa, wato yawansu manya da kanana ya kai goma ko fiye. Don samun kaso mafi girma na mallakar iko da dukiyoyi a shiyyar Darfur a nan gaba, kungiyoyi daban daban ba su sami ra'ayi daya a kan sharudan da gwamnatin Sudan ta gabatar don yin shawarwarin shimfida zaman lafiya ba. A gun taron duniya da aka kira a ranar 3 ga wannan wata a birnin Arusha kan batun Darfur na kasar Sudan, ta hanyar yin tattaunawa cikin wasu kwanaki, shugabannin rukunoni daban daban masu yin adawa da gwamnati wadanda suke halartar taron sun sami ra'ayi daya, a shirye suke za su yi shawarwarin siyasa da gwamnatin Sudan tun da wurwuri bisa matsayinsu daya da bukatarsu daya, kungiyoyi daban daban masu adawa da gwamnati su ma sun sami ra'ayi daya a kan taswirar shimfida zaman lafiya a Darfur da shawarwarin da za a yi a nan gaba, sun sake jadadda cewa, suna son aiwatar da alkawarin da suke yi na dakatar da aikace-aikacen yin adawa da juna, kuma za su maraba da rundunar sojojin hadin guiwa da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afrika suka tura zuwa shiyyar Darfur. Ta hakan, an shimfida hanyar yin shawarwarin zaman lafiya da gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnatin za su yi a tsakaninsu don shimfida zaman lafiya.

A duk tsawon lokacin taron, kakakin kungiya mafi girma ta yin adawa da gwamnati da ke shiyyar Darfur wato kungiyar neman adalci da zaman daidai wa daida Mr Ahmed Hussein Adam ya bayyana cewa, yawancin kungiyoyin da ke halartar taron Arusha suna da buri irin daya sosai na hakika, wato ci gaba da yin iyakacin kokarinsu don shimfida zaman lafiya a shiyyar Darfur ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. A ganinsa, taron na da abu mai yakini,kuma zai ba da taimako ga dinkuwar matsayin bangarori daban daban da daidaita shi a gun shawarwarin da za su yi da gwamnatin Sudan. Bisa sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afrika suka bayar bayan taron, an ce, kungiyoyi daban daban masu yin adawa da gwamnati wadanda suke halartar taron sun karfafa cewa, bai kamata ba a daidaita rikicin Darfur ta hanyar yin amfani da karfin makamai, a akasin haka ya kamata a daidaita batun ta hanyar siyasa. A lokacin da za su yi shawarwarin karshe da gwamnatin Sudan, ya kamata kungiyoyi daban daban su daddale wani dayantaccen tsari wajen raba iko da dukiyoyi da tsara matakan tsaro tare da batun yankunan kasa da na jinkai da dai sauransu.

Amma Abin da ke jawo hankulan mutane shi ne, muhimmiyar kungiya mafi girma da ke yin adawa da gwamnati da ke shiyyar Darfur wato kungiyar neman kwatar 'yancin Sudan ba ta aika wakilai don halartar taron ba.

A gun bikin rufewar taron, manzon musamman na Majalisar dinkin duniya kan batun Darfur Jan Eliasson ya bayyana cewa, don wakiltar dukan bangarori, sakamakon da aka samu a gun taron zai karbi ra'ayoyin kungiyoyi masu adawa da gwamnati wadanda ba su halarci taron ba.

Manazartan al'amarin sun bayyana cewa, ba a iya daidaita matsaloli da yawa da suke da nasaba da shiyyar Darfur ta hanyar kiran wani taro kawai ba.

Bayan taron, Jan Eliasson zai tafi birnin Kartoum a ranar 7 ga wannan wata don yin shawarwari da gwamnatin Sudan, sa'anan kuma zai tafi shiyyar Darfur, Mr Salim Ahmed Salim shi ma zai tafi birnin Kartoum da shiyyar Darfur a mako mai zuwa.(Halima)