Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 14:46:59    
Rundunar sojan kasar Sin ta isa wurin da za a gudanar da atasayen soja na hadin gwiwa mai suna "manzancin zaman lafiya-shekarar 2007"

cri

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana, an ce , ran 1 ga wata da yamma , rundunar sojan kasar Sin da ta halarci atasayen soja na hadin gwiwa mai suna "manzancin zaman lafiya-shekarar 2007" ta isa wurin da za a gudanar da atasayen soja na hadin gwiwa .

Rundunar sojan kasar Sin da ta isa wurin na karo na farko ta hada da sojoji da hafsoshi kimanin dari biyu wadanda suka zo daga rundunar sojan kasa da ta sama . Kawo yanzu dai , yawan sojojin kasar Sin da suka isa yankin atasayen sojan kasar Rasha ya kai kusan dubu daya .

Ban da wannan kuma , rundunonin sojan jiragen sama masu saukar ungulu na kasar Sin da suka halarci atasayen soja na hadin gwiwa duk sun isa yankin atasayen kasar Rasha .

Wannan shi ne karo na farko da sojojin kasar Sin suka je kasar Rasha can nesa don halartar atasayen sojan suka yi marabtar zuwan ranar taya murnar kafuwar rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin a sansanin kasar waje .

Kwana daya da ya wuce da dare , bangaren kasar Rasha ya kira wata liyafa don taya rundunar sojan kasar Sin murnar cika shekarun 80 da kafuwar rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin .(Fatima)