Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 14:06:09    
Kusoshin kasar Sin sun halarci bikin murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojojin jama'ar Sin

cri

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana labari cewar, jiya ranar 1 ga wata da dare, shugabannin kwamitin soja na tsakiyar Sin tare da wakilan da suka halarci babban taron wakilan jarumai da na sojoji abin koyi na rundunar sojan Sin baki daya sun shirya bikin murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin. Mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiyar Sin Mr. Guo Boxiong da ministan tsaron kasa Mr. Cao Gangchuan sun halarci bikin.

A gun bikin, mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiyar Sin Mr. Xu Houcai ya bayar da jawabi inda ya furta cewar, rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin wata rundunar jama'a ce da ke fitar da jarumai masu tarin yawa zuriya bayan zuriya. A cikin tarihi mai haske na shekaru 80, an bullo da jarumai da sojoji abin koyi da nagartattun rukunnonin da ba a iya kirga su ba wadanda suka zubar da jini da gumi da kuma yi namijin kokarinsu wajen sha'anin juyin-juya-hali da ayyukan gina kasa da yin gyare-gyare, haka kuma sun ba da babban taimako ga sha'anin gina rundunar sojan jama'a da raya ta.

Ya kuma kara da cewa, ya kamata duk rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin su cigaba da kara karfin yada kyawawan al'adunsu iri na bin umurnin jami'yyar kwaminis ta Sin da bauta wa jama'a da nuna jaruntaka don yin yaki, su kuma kokarta wajen ciyar da aikin gina rundunar soja gaba da kyau kuma cikin sauri ta yadda za ta kara samar da sabuwar gudummowarta ga aikin aiwatar da nauyin da ke bisa wuyanta a cikin sabon mataki na sabon karni.(Murtala)