Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-02 13:59:49    
An shirya liyafa a Ofisoshin jakadanci da ke a kasashe daban daban don murnar ranar bikin kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin

cri
A ran 1 ga wata, an shirya liyafa a ofisoshin jakadancin Sin da ke a kasar Jamus da kasar Zimbabwe da kasar Kazakhstan don murnar ranar cika shekaru 80 da kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin. A ran 31 ga watan jiya, an shirya liyafa a ofishin jakadanci a kasar Kyrgyzstan don murnar ranar bikin kafa rundunar sojojin kwatar 'yancin jama'ar kasar Sin.

A gun liyafar hafsan diplomasiya na kasar Sin da ke kasar Zimbabwe Tian Jianjun ya ba da jawabi cewa, abokantaka na sha'anin soja tsakanin kasar Sin da kasar Zimbabwe da abokantaka a tsakaninsu suna da dangantaka sosai. Hadin kai da mu'amalar da ake yi tsakanin sojojin biyu a cikin bangarori da yawa ta kara dankon zumuncin da ke a tsakanin kasashen biyu. Babban ma'aikacin hukumar tsaron kasa na kasar Zimbabwe da ya halarci wannan liyafa, ya nuna cewa, yana fatan abokantaka tsakanin kasashen biyu da sojojin biyu za ta ci gaba har abada.

A gun liyafa daban kuma, hafsan diplomasiya na kasar Sin da ke kasar Jamus manjo janar Zhang Mingzhong ya nuna cewa, dangantakar hadin kai tsakanin sojan kasar Jamus da sojan kasar Sin ta samu kyakyawa sakamako, kuma za ta samu ci gaba sosai. Ma'aikacin sojan kasar Jamus ya nuna cewa, yana fatan dangantakar hadin kai tsakanin kasashen biyu da sojojin biyu za ta kara ci gaba.(Abubakar)