Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 11:51:36    
Kasar Sin tana murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin

cri

Yau ran 1 ga watan Augusta rana ce ta murnar kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin. A wannan rana, jaridar People's Daily ta ba da wani sharhi domin murnar cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan kasar Sin.

Sharhin ya bayyana cewa, a sakamakon yin gwagwarmaya ba tare da kasala ba na tsawon shekaru 80, rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin ta fito kanta da wata hanya da ke dacewa da halin da kasar Sin ke ciki a zahiri a fannin raya sojan jama'a, ta samar da ka'idoji da hanyoyi da dabara masu tsarin musamman na kasar Sin game da raya soja da gudanar da harkokin soja. Sa'an nan kuma, ta horar da nagartattun kwararru masu ilmin aikin soja da yawa, ta kuma samar da tunanin Mao Tse-tung a fannin aikin soja da tunanin Deng Xiaoping a fannin bunkasa rundunar soja a sabon lokaci, da kuma tunanin Jiang Zemin a fannin tsaron kasa da bunkasa rundunar soja.

Dadin dadawa kuma, sharhin ya ce, a halin yanzu, rundunar sojan kasar Sin tana cikin sabon mafarin tarihi wajen samun bunkasuwa. Rundunar sojan kasar Sin na daukar nauyin tarihi a sabon karni a cikin sabon mataki. Tabbas ne sojojin kasar Sin jarumai za su samu sabbin nasarori wajen kiyaye moriyar Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jama'ar Sin da karewa da raya kasar Sin da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya, a karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda malam Hu Jintao ke shugabansa.(Tasallah)