Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-23 18:21:24    
Rundunar kasar Sin tana yin hadin gwiwa da kasashen waje a fannin yaki da ta'addanci

cri
Ran 1 ga watan Agusta na wannan shekara rana ce ta cikon shekaru 80 da kafuwar rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin. Tun daga ran 9 zuwa ran 17 ga wata mai zuwa, sojojin kasashe mambobin Kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za su yi rawar daji ta 'zaman lafiya-2007' cikin hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci a kasashen Sin da Rasha. Kwararrun kasar Sin masu ilmin aikin soja sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan cewa, sojojin kasar Sin da na kasashen waje suna fadada fannonin yin hadin gwiwa ta fuskar yaki da ta'addanci da kuma zurfafa irin wannan hadin gwiwa.

A shekarun baya da suka wuce, rundunar sojan kasar Sin tana yin hadin gwiwa da kasashen waje domin yaki da 'yan ta'adda cikin himma da kwazo, ta sami amincewa sosai daga gamayyar kasashen duniya, ta kuma sami sakamako mai kyau daga wuraren da ke makwabtaka da kasar Sin. Rawar daji ta 'zaman lafiya-2007' da za a yi cikin hadin gwiwa domin yaki da 'yan ta'adda a nan gaba ba da dadewa ba rawar daji ce mafi girma da za a yi bayan kafuwar kungiyar yin hadin gwiwa ta Shanghai, haka kuma, wannan shi ne karo na farko da sojojin kasar Sin na rundunoni daban daban za su yi rawar daji mai girman haka kuma mai dogon zango a ketaren kasa da kasa. A lokacin da yake zantawa da wakilinmu a kwanan baya, malam Zheng Shouhua, wani manazarci na cibiyar nazarin ilmin aikin soja ta rundunar sojan 'yantar da jama'a ta kasar Sin, ya kiyasta cewa, sojojin kasar Sin da na kasashen waje za su fadada fannonin yin hadin gwiwar yaki da ta'addanci, za su kuma kyautata irin wannan hadin gwiwa. Ya ce,'In muna cewa, a can da, sojojin kasar Sin da na kasashen waje sun fi mai da hankulansu kan kara fahimtar juna da yin cudanya a tsakanin bangarori 2 ko bangarori daban daban a fannin yaki da ta'addanci, sa'an nan kuma, sun yi yaki da ta'addanci bisa tsarin yin mu'amala da juna. To, ma iya cewa a nan gaba za su kara yin mu'amala a fannonin leken asiri da ba da jagoranci da daukar matakai da fasaha da ilmi. Yawan kasashen da za su yi irin wannan mu'amla zai yi ta karuwa.'

Wannan kwrarre yana ganin cewa, gwamnatin Sin da sojojin kasar Sin suna yin hadin gwiwa da kasashen waje a fannin yaki da ta'addanci cikin himma da kwazo, sun taka babbar rawa a fannin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda na kasa da kasa.

Amma malam Zheng ya nuna cewa, nan gaba za a kyautata zurfin rawar daji, za a kuma gwabza rawar daji a zahiri, ban da wannan kuma, za a yi dabarori daban daban wajen yin rawar daji, ta haka, za a kara sami kyakkyawan sakamako daga rawar daji.

A shekarun baya da suka wuce, kungiyoyin 'yan ta'adda na kasa da kasa sun gama kansu domin kafa tsare-tsarensu na yin aikace-aikacen ta'addanci a ketaren kasa da kasa. Shi ya sa, da kyar sojojin wata kasa kadai su ci nasarar yaki da ta'addanci. Malam Zheng ya kara da cewa,'Kasar Sin ba za ta san ci gaban aikace-aikacen ta'addanci cikin lokaci ba, sai ita da kasashen duniya sun kafa kyakkyawan tsarin more rahotannin asiri tare. Kasar Sin ba za ta iya murkushe 'yan ta'adda ba, ba za ta iya kai musu hari a duk inda suke ba, sai ita da kasashen duniya, musamman ma kasashen da ke makwabtaka da ita sun hada gwiwarsu, su kuma samar da babban tsarin yaki da ta'addanci a tsakaninsu ko kuma a tsakanin yankuna.'

Malam Zheng ya ci gaba da cewa,'Rundunar sojojinmu ta sami kyawawan fasahohi da yawa daga wajen yin mu'amala da kasashen waje da sojojinsu, ta sa kaimi kan kyautatuwar ilmin yaki da ta'addanci da kuma aikin horo ta fuskar aikin soja, ta kuma karfafa raya tsarin sojoji da kayayyakin soja na yaki da ta'addanci, ta haka, karfin rundunar sojan kasarmu a fannin yaki da 'yan ta'adda ya sami kyautatuwa sosai.'

A bayyane ne a sakamakon yin cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasashen duniya, karfin kasashen duniya a fannin yaki da 'yan ta'adda zai ci gaba da samun kyautatuwa, sa'an nan kuma, tabbas ne za a kara kai bugu mai karfi ga ta'addancin da ke kawo wa dukkan dan Adam illa.(Tasallah)