Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-18 15:17:05    
Beijing ba ta gamu da matsala ba wajen gina filaye da dakunan wasa domin taron wasannin Olympic na shekarar 2008

cri

Kowa ya sani cewa, ba a iya raba filaye da dakunan wasa masu inganci daga aikin shirya wata gasar wasannin motsa jiki ba. A yayin da birnin Beijing yana share fage ga taron wasannin Olympic na shekara ta 2008, gina filaye da dakunan wasa na ta jawo hankulan mutane sosai.

A gun taron manema labaru da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kira a ran 11 ga watan Yuli, jami'in kula da ayyukan taron wasannin Olympic na Beijing kuma babban injiniya na ofishin jagorancin ayyukan taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 na Beijing malam Wu Jingjun ya yi wa kafofin yada labaru karin bayanin cewa, yanzu ana gina filaye da dakunan wasa domin taron wasannin Olympic na Beijing kamar yadda ya kamata. Bayan da aka soma gina filayen wasa 2 na wucin gadi, wato na wasan Triathlon da ke kunshe da iyo da gudun fanfalake da kuma tseren keke da kuma na tseren keke a kan hanyar mota a birnin, a watan Afril na wannan shekara, Beijing ta fara gina dukkanin filaye da dakunan wasa guda 31 da gine-gine guda 5 da abin ya shafa. Sa'an nan kuma, a cikin dukkan filaye da dakunan wasa guda 45 masu zaman kansu domin aikin horo, ta soma gina wasu 43.Ya ce,'Beijing ta kaddamar da gina dukkan filaye da dakunan wasa guda 31 da gine-gine guda 5 da abin ya shafa. Ban da filin wasan kwallo mai laushi na Fengtai da ta gama gina shi a shekarar bara, yanzu ta riga ta kawo karshen gina yawancin muhimman gine-gine na wadannan filaye da dakunan wasa da kuma gine-ginen da abin ya shafa, tana yi musu ado da kuma ajiye injunan wutar lantarki, ta kusan kammala wasu ayyuka.'


1 2 3